‘Yan bindiga sun kashe mutane 9 sannan wasu mutum uku sun ji rauni a harin da suka kai a kauyen Avu Kwall dake karamar hukumar Bassa, Jihar Filato.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Alabo Alfred ya ce rundunar ta aika da jami’an ta domin Samar da tsaro da kiyaye doka a kauyen tare da fara gudanar da bincike.
Wani mazaunin kauyen Likita Dani ya ce maharan sun afka kauyen a daren ranar Lahadi yayin da mutane ke barci.
“Mun kira jami’an tsaro domin su kawo mana dauki amma ba su zo ba sai ranar Litini da safe.
“Mun kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da samar da tsaro a yankin mu.
A shekarar bara mutane da dama sun rasa rayukansu a dalilin rikicin makiyaya da manoma a kananan hukumomin Barkin Ladi, Mangu da Riyom a jihar.
Wasu da dama sun rasa gidajen su na zama inda a cikin wannan watan ne wasu ke dawowa gidajen su saboda zaman lafiyan da aka samu a yankin.
Discussion about this post