Kan Majalisar Ɗinkin Duniya ya rabu gida biyu a ranar Litinin, yayin da mambobin su ka kasa amincewa da matsaya ɗaya dangane da tayin tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Gaza.
Ranar Litinin ɗin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kaɗa ƙuri’a kan tayin da Rasha ta yi na tsagaita wuta a Gaza, dangane da yadda lamarin yaƙin ya shafi farar hula.
Ganin yadda tayin tsagaita wutar ya raba kan Zauren Majalisar, sai ba a yi amfani da tayin wanda Rasha ta yi ba.
Da a ce an yi amfani da tayin na Rasha, to da an tilasta wa ɓangarorin biyu su tsagaita wuta, a sako waɗanda aka yi garkuwa da su, sannan kuma a bada damar kai kayan agaji a yankin Gaza, yankin da mako ɗaya kenan Isra’ila na ci gaba da kai masa hare-haren luguden bama-bamai.
Daga cikin mambobin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya, biyar ne kaɗai da suka haɗa da Chana, Gabon, Mozambique, Rasha da UAE suka goyi bayan Rasha.
Huɗu kuma da suka haɗa da Faransa, Japan, Ingila da Amurka ba su amince ce ba.
Yayin da shida da suka haɗa da Albaniya, Brazil, Ecuador, Ghana, Malta da Switzerland ba su shiga kaɗa ƙuri’ar ba.
Ƙasashe huɗu da suka ƙi amincewa duk manyan ƙasashen G7 ne, kuma mafi kusancin dangantaka da Isra’ila. Kuma Mambobin Dindindin na Majalisar Tsaro ta Ɗinkin Duniya.
Kafin a kai ga amincewa da tilasta tsagaita wutar, tilas sai tayin na Rasha ya samu ƙuri’u 9 daga ƙasashe daban-daban.
An ruwaito cewa wakiliyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield na cewa sun ƙi yarda da tayin Rasha, saboda Rasha ɗin ta ƙi yin Allah wadai da hare-haren da Hamas ta fara kaiwa Isra’ila.
Ta ce ƙin yin Allah wadai da hare-haren Hamas, tamkar ɗaure wa ta’addanci gindi ne kan Isra’ila Rasha ɗin ke yi.
Discussion about this post