Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Olanipekun Olukoyede matsayin Shugaban Hukumar EFCC, a wani ƙarfa-ƙarfan naɗin da ya karya dokar EFCC.
Shugaban ƙasa ɗin ya amince da naɗin Muhammad Hammajoda matsayin Sakataren EFCC, wanda zai shafe shekaru biyar a kan muƙamin.
Dukkan naɗe-naɗen dai ba za su tabbata ba, har sai Majalisar Dattawa ta amince tukunna.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale ne ya fitar da sanarwar naɗin a yau Alhamis.
Hakan ya tabbatar da rahoton musamman da PREMIUM TIMES ta buga a ranar Litinin cewa Tinubu zai naɗa wanda bai cancanta ba a shugabancin EFCC.
A labarin, Tinubu ya shirya gadangarƙamar naɗa Olukoyede, wanda bai cika sharuɗɗan shugabancin EFCC ba.
Idan dai ba yanzu-yanzu ko kuma nan gaba kaɗan Shugaba Bola Tinubu ya canja tunani ba, to ko shakka babu zai naɗa Olanipekun Olukoyede shugabancin Hukumar EFCC.
Idan kuwa har Tinubu ya naɗa shi, to fa zai jangwalo tashin-ballin ƙorafe-ƙorafen rashin cancantar shi Olukoyede ɗin ya shugabanci EFCC.
Olukayode wanda lauya ne, ya taɓa riƙe muƙamin sakataren EFCC tsawon shekaru biyu, a lokacin shugabancin Ibrahim Magu a EFCC.
Idan kuma za a tuna, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Magu ne cikin 2020, tare da Olukayode, kuma har yau ba a sake maida su ba.
Kafin Olukayode ya zama sakataren EFCC, ya riƙe muƙamin shugaban ma’aikata na EFCC, a ƙarƙashin Magu.
Wata majiyar PREMIUM TIMES ta bayyana cewa, “Shugaba Bola Tinubu ya shirya tsaf domin naɗa Olanipekun Olukoyede shugabancin Hukumar EFCC.” Haka dai majiyar mu da ke cikin Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar, domin ta na da masaniyar.
Sai kuma majiyar ta roƙi kada wannan jarida ta buga sunan ta.
Haka nan kuma dai wata majiyar ta ƙara tabbatar da wannan shiri da Tinubu ke yi, wadda ko bayan naɗin sa, to sai idan Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sa ɗin.”
Cikin watan Yuni ne Shugaba Tinubu ya dakatar da tsohon Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, a madadin sa kuma, sai ya naɗa Abdulkarim Chukkol shugabancin riƙon EFCC ɗin.
Kafin naɗin sa, Chukkol shi ne Daraktan Ayyukan EFCC.
Watanni huɗu kenan Bawa na tsare a hannun SSS, har yau ba sa sake shi ba, tun bayan da suka gayyace shi amsa tambayoyi a ranar da aka dakatar da shi.
Ana raɗe-raɗin cewa Bawa ya amince zai sauka daga muƙamin sa.
Wane Ne Olanipekun Olukoyede?:
Ɗan asalin Jihar Ekiti ne, kuma an haife shi cikin 1969. A yau ya na da shekaru 54 kenan.
Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya naɗa shi Sakataren EFCC a cikin 2018.
Sai dai kuma an samu ruɗani yayin naɗa Olukoyede, yayin da wani sanata mai suna Isa Misau ya zargi Shugaban Kwamitin Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, na Majalisar Dattawa, Sanata Chukwuka Utazi da laifin ware wasu mambobin kwamiti wajen shirya rahoton wanke Olukoyede domin a naɗa shi Sakataren EFCC.
Olukoyede lauya ne da ya taɓa yin aiki a ofishin aikin lauyanci na tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, kafin a naɗa shi Sakataren EFCC.
Shin Olukoyede Ya Cancanta Riƙe Shugabancin EFCC?:
Idan har aka amince da naɗin sa, zai zama ɗan kudu na farko da zai riƙe EFCC.
Sai ana ganin cewa Olukoyede bai cika wasu sharuɗɗan naɗa shi shugabancin EFCC ba.
Sashe na 2(3) na Dokar EFCC ta 2005, ta nuna cewa sai wanda ke kan aikin jami’in tsaro ko wanda ya rigaya ya yi ritaya ne kaɗai za a iya naɗawa shugabancin EFCC.”
Sannan kuma ya kasance mutsayin da ya ke a lokacin na zai kasa ga Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ba, ko wani muƙamin makamancin haka a wasu ɓangarori na hukumomin tsaro.
“Kuma ya kasance ya shafe aƙalla shekaru 15 ya na aiki.”
Olukoyede dai bai kai shekaru 15 ya na aiki a EFCC ba, kuma bai taɓa yin aikin ɗamara ba.
Shi kuma Tinubu da ke ƙoƙarin naɗa shi, tuni aka fara kukan cewa bai kamo hanyar kawo gyara a ƙoƙarin daƙile cin hanci da rashawa ba.
Discussion about this post