Shugaban Kasa Bola Tinubu ya aika da sunan Abba Balarabe majalisar Dattawa domin a tantance shi ya zama ministan Najeriya.
Idan ba a manta ba majalisar dattawa ta ki amincewa da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya zama minista bisa dalilan wasu korafe korafe da aka mika wa majalisar.
Sai dai kuma daga baya ma El-Rufai ya ce ya hakura da da kujerar ministan.
Tinubu ya aika da sunan Abbas Balarabe a matsayin wanda zai cike gurbin Kaduna a majalisar Zartaswar kasa.
Discussion about this post