Duk da kukan rashin kuɗi da taɓarɓarewar tattalin arzikin da Gwamnatin Tarayya ke fuskanta, har ta kai an cire tallafin fetur, Shugaba Bola Tinubu ya ƙara yawan jami’an yaɗa labaran sa, waɗanda ya ƙirƙiro wa muƙamai daban-daban.
Tinubu ya naɗa garke guda na jami’an yaɗa labarai, daidai lokacin da ake ta kiraye-kirayen cewa ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta rage yawan kashe kuɗaɗe barkatai.
A ranar Litinin ce Shugaba Tinubu ya ƙara naɗa mutum biyar a cikin garken jami’an yaɗa labaran sa, wato Garken Masharwatan Shugaban Ƙasa a Fannin Yaɗa Labarai, waɗanda a yanzu yawan su ya kai su 11 kenan.
Cikin wata sanarwar da Mashawarci na Musamman Kan Yaɗa Labarai ga Shugaban Ƙasa, wato Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana sunayen waɗanda aka yi wa sabbin naɗe-naɗen da Fela Durotoye, Frederick Nwabufo da Linda Akhihbe.
Sauran sun haɗa da Aliyu Audu da Francis Abah.
Akwai kuma Akhigbe wadda kafin naɗin ta ita ce babbar wakiliyar Gidan Talabijin na Channels a Fadar Shugaban Ƙasa, wadda a yanzu aka naɗa ta Mai Bada Shawara a Fannin Sadarwa ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin ECOWAS.
Shekaranjiya ne kuma Seyi Tinubu ɗan Shugaba Tinubu ya kinkimi jirgin Shugaban Ƙasa ya tafi Kano da shi kallon wasan Polo.
Haka nan kuma an yi mamakin yadda Tinubu ya naɗa Ministoci har 48, a daidai lokacin da ya fi kowa kukan gwamnati na neman hanyoyin da za ta faɗaɗa samun kuɗaɗen shiga.
Rundunar Sojojin Baka: Garken Dakarun Yaɗa Labaran Shugaba Tinubu:
1. Ajuri Ngelale (Special Adviser Media and Publicity)
2. Tunde Rahman (Senior Special Assistant to the President — Media)
3. Abdulaziz Abdulaziz (Senior Special Assistant to the President — Print Media)
4. O’tega Ogra – (Senior Special Assistant (Digital/New Media)
5. Tope Ajayi – Senior Special Assistant (Media & Public Affairs))
6. Segun Dada (Special Assistant — Social Media)
7. Nosa Asemota – Special Assistant (Visual Communication)
8. Mr Fela Durotoye (Senior Special Assistant to the President — National Values & Social Justice)
9. Mr Fredrick Nwabufo (Senior Special Assistant to the President — Public Engagement)
10. Mrs Linda Nwabuwa Akhigbe (Senior Special Assistant to the President — Strategic Communications)
11. Mr Aliyu Audu (Special Assistant to the President — Public Affairs)
Discussion about this post