Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta soke nasarar da zaɓen fidda-gwani na takarar gwamnan Jihar Bayelsa da Timipre Sylva ya samu.
Sylva wanda shi ne Ƙaramin Ministan Harkokin Fetur a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, shi ne APC ta tsaida a takarar zaɓen wanda za a yi cikin watan Nuwamba.
Ya samu nasarar ce a zaɓen fidda-gwanin da APC ta shirya cikin watan Afrilu.
Ya samu ƙuri’u 52,061, inda ya doke abokan takarar sa, da suka haɗa da Joshua Machiver, Festus Danumiebi, Maureen Etebu, David Lyon da Isikima Johnson.
A ranar 11 Ga Nuwamba ce za a yi zaɓen gwamna a wasu jihohin da su ka haɗa da Bayelsa da Kogi.
Mai Shari’a Donatus Okorowo na Babbar Kotun ne a ranar Litinin, ya ce Sylva bai cancanci tsayawa takara ba, bisa la’akari da hujjojin da wani ɗan jam’iyyar APC mai suna Demesuoyefa Kolomo ya shigar a kotun.
Kolomo ya ce a baya Sylva an rantsar da shi sau biyu a matsayin gwamna a Jihar Bayelsa. Ya yi shekara ɗaya ya na gwamna kuma ya yi shekara huɗu.
Ya ce Dokar Najeriya ta 1999, ta haramta a rantsar da mutum fiye da sau biyu a matsayin gwamna.
Sylva wanda ya yi gwamna a 2007 da kuma 2011 a matsayin Gwamnan Bayelsa, ƙarƙashin PDP. Amma daga baya ya koma APC, har Buhari ya naɗa shi Ƙaramin Ministan Harkokin Fetur.
Idan Sylva da APC suka ɗaukaka ƙara amma ba su yi nasara har a Kotun Ƙoli ba, to APC ba ta da ɗan takara kenan a zaɓen gwamnan Bayelsa.
Tuni dai APC ta ce ba ta amince da sakamakon hukuncin ba, don haka za ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Discussion about this post