Shugaban Muryar Najeriya (VON), Osita Okechukwu ya roƙi ‘yan Najeriya su yi kaffa-kaffa da irin fafutikar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ke yi don ya ga lallai sai ya yi mulkin Najeriya.
Okechukwu ya bayyana haka a ranar Litinin, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, dangane da takardun shaidar karatun da Jami’ar Chicago ta Amurka na Shugaba Bola Tinubu, ta damƙa wa Atiku.
Tun bayan sakin takardun dai wasu mutane suka riƙa cewa sun lura akwai bambanci tsakanin tsakanin Satifiket ɗin da Atiku ya damƙa wa INEC a lokacin da ya fito takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin APC.
Okechukwu ya ce Atiku ba shi da martabar da zai riƙa haƙiƙicewa ya ce sai an bi tsarin doka sau da ƙafa.
Ya ce tabbatuwar Najeriya a ga ta samu ta ɗore kan tafarkin dimokraɗiyya shi ne mafi muhimmanci, musamman idan aka yi la’akari da matsalar da yadda masu ƙoƙarin daƙile dimokraɗiyya ke ta ƙasa bayyana a Afrika ta Yamma.
“Gaskiya ba so na ke yi ta maganar ba. Amma wane mutunci ke ga dattijon da ya yi fatali da tsarin karɓa-karɓa, ya karya dokar jam’iyya, ya danne damar wani yanki, kuma shi ne yanzu zai ce wai dole sai an bi tsarin da doka ta gindiya.
“Ai ya kamata ya san cewa mai bunu a gindi ba ya kai gudummawar kashe gobara.
“Mu yanzu abin da ‘yan Najeriya ke buƙata dangane da batun takardun Chicago shi ne mu samu dimokraɗiyyar nan ta ɗore, musamman idan muka yi la’akari da abin da ke faruwa a Afrika ta Yamma, inda dimokraɗiyyar ke ta faman fuskantar barazana.”
Osita ya ce shi kan sa Atiku ai ya karya tsarin dokar PDP kafin ya fito takara, kuma ya karya yarjejeniyar tsarin karɓa-karɓa.
“Kuma kada mu manta, Atiku ne ya haifar da nasarar Tinubu, domin shi ya raba kan PDP, yayin da ya karya dokar tsarin PDP ya fito takara, kuma ya ƙi mutunta karɓa-karɓa. Hakan da Atiku ya yi kuwa ya nuna shi ba mai kishin haɗin kan Najeriya da ‘yan Najeriya baki ɗaya ba ne.” Cewar Osita.
Osita ya nemi Atiku ya daina gaganiyar sai ya yi mulki bakin-rai-bakin-fama, kuma ya nemi gafarar ‘yan ƙabilar Igbo, waɗanda suka rungumi PDP shekara da shekaru, amma da lokacin fitowar su takara ya yi, sai Atiku ɗin ya yi masu ƙafar ungulu.
Discussion about this post