Shugaba Bola Tinubu ya bayyana shirin gaggawa na yin ƙarin albashin wucin-gadi na watanni shida a jere ga masu ƙaramin albashi.
A cikin jawabin sa ga al’ummar Najeriya a safiyar Lahadi, ranar 1 Ga Oktoba, wadda ke daidai da cika cika shekaru 63 da samun ‘yanci, Tinubu ya ce gwamnatin sa ta kamo hanyar rage raɗaɗin tsadar rayuwa, ta hanyar yi wa masu ƙaramin albashi ƙari na wucin-gadin watanni shida a jere.
Ya ce masu ƙaramin albashi za su samu ƙarin Naira 25,000 a kowane wata, har tsawon watanni shida a jere.
Da ya ke taɓo batun matsanancin halin raɗadin tsadar rayuwa da aka shiga tun bayan cire tallafin fetur, Tinubu ya ce, “Ban so Najeriya ta afka cikin raɗaɗin ƙuncin da ake fama da shi ba”.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa a matsayin sa na Shugaban Ƙasa, ba ya farin ciki da jin daɗin jagorantar al’ummar da ke fama da mawuyacin halin da ake fuskanta yanzu a ƙasar nan.
A jawabin sa a yau Lahadi domin tunawa da zagayowar ranar samun ‘yancin ƙasa, shekaru 63 da suka gabata, Tinubu ya ce, “ina ma a ce ba a shiga cikin mawuyacin halin da ake fuskanta yanzu a ƙasar nan ba.”
A jawabin na sa, ya ce tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasa da gwamnatin sa ta bijiro da su masu kaifi da zafi da ƙunci ne. To amma fa wannan kaɗai ce hanyar da za a iya bi nan gaba kaɗan a cimma sauƙi da walwala da yalwar arziki.
Ya ce ‘yan Najeriya nagartattun mutane ne, “dukkan mu daidai da juna m ke, babu wani da ya fi wani a cikin mu. Nasarar da Najeriya ta samu ce za ta iya tantance mu.”
Tinubu ya ce raɗaɗin ƙunci da tsadar rayuwa da ake ciki a yanzu ba mai ɗorewa ba ne dimun-da’imun. Ya ce “nan gaba kaɗan wannan wahala za ta zama tarihi.”
Da ya koma kan alƙawurran da ya yi a farkon mulkin sa, Tinubu wanda a yau ya cika watanni huɗu kan mulki, ya ce ya yi alƙawarin sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya, tare da zamanantar da shi. Kuma ya yi alƙawarin kare rayukan ‘yan Najeriya da su da dukiyoyin su.
“Na ɗauki gaban-gabarar cire tallafin fetur ba don ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya wahala ba, sai don samar masu rayuwa mai sauƙi da yalwar arziki nan gaba ba da daɗewa ba.
“Saboda haka ina gani da ido na, kuma ina ji da kunne na irin mawuyacin halin da ake ciki. Roƙo na shi ne a ƙara juriya, za a fita daga wannan ƙunci a shiga cikin walwala.” Inji Tinubu.
Discussion about this post