Kotun Amurka ta ƙi amsa roƙon da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi, wanda ya roƙe ta kada ta bai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar kwafen takardun bayanan karatun shaidar Difiloma ɗin da Tinubu ya yi iƙirarin ya samu a jami’ar.
Mai Shari’a Nancy Maldonado, ta umarci Jami’ar Chicago ta gaggauta damƙa wa lauyoyin Atiku Abubakar kwafen takardun shaidar Tinubu a cikin sa’o’i 48.
Ta yanke hukuncin a ranar Asabar, inda ta ce a gaggauta ba su takardun kada a wuce ranar Litinin da rana.
Maldonando ya haddada hukuncin da Mai Shari’a Jeffery Gilbert na Kotun Majistare ya yanke a ranar 20 Ga Satumba, wanda ya ƙi amsa roƙon Tinubu, ya umarci a damƙa wa Atiku kwafen takardun.
‘Atiku Zai Min Illa Idan Jami’ar Chicago Ta Tamƙa Masa Kwafen Takardu Na’ – Tinubu:
Bayan Atiku ya nemi kotu ta umarci Jami’ar Chicago ta ba shi kwafen takardun na Tinubu, sai shi ma Tinubu ya garzaya kotun, ya roƙi cewa kada a ba Atiku takardun.
A lokacin, Shugaba Bola Tinubu ya ƙara matsa lambar ganin cewa ya yi duk ƙoƙarin da zai yi, don ya ga Kotun Amurka ba ta bada umarni ga Jami’ar Chicago ta bayar da kwafen satifiket ɗin karatun sa ga Atiku Abubakar ba.
Bayan Tinubu ya karɓi hukuncin da Kotun Gundumar Arewacin Illinois ta yanke, cewa ta dakatar da umarnin a damƙa kwafen takardun shaidar Tinubu ga Atiku, sai kuma Tinubu ya sake shigar da wani ba’asi, inda ya roƙi kotu cewa ba ya so a damƙa kwafen satifiket ɗin ga Atiku kwata-kwata.
Lauyan Tinubu da ke zaune Amurka, mai suna Oluwole Afolabi ne ya shigar da riƙon a madadin Tinubu, bisa dalilai biyu da ya gabatar wa kotun.
Na farko dai ya ce ko an damƙa wa Atiku Abubakar satifiket ɗin TInubu da sauran kwafe-kwafen takardun makarantar sa, ba za su amfana masa da komai ba a kotun Najeriya.
Dalili na biyu kuma cewa ya yi, idan aka damƙa wa Atiku kwafe-kwafen takardun makarantar Tinubu, to an ba shi lasisi ne na shiga gonar da ba tasa ba, domin laluben sirrin wani wanda shi ma doka ta hana a bai wa wani ƙofar shiga ya binciki sirrin rayuwar sa.”
Ya roƙi kotu ta yi watsi da buƙatar Atiku kawai.
“Ko ma an damƙa takardun, babu abin da za su tainana masa, sai kawai don ya na ɗan adawa ne, zai yi bincike kan wani sirrin abokin adawar sa.”
Tinubu ya ce “za a yi min illa idan aka sakar wa Atiku takardun shaidar karatu na a Jami’ar Chicago.”
Ya ce a baya ai Atiku ya samu kwafen, amma ta bayan fage, kuma ya riƙa ragargaza sa a kan su.
Ya ƙara cewa ba gaskiya ba ce da Atiku ya ce Kotun Ƙoli a Najeriya za ta iya amfani da kwafen takardun wajen yanke hukunci a ƙarar zaɓen 2022 da Atiku ya shigar.
A makon jiya dai PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa kotun Amurka ta umarci Jami’ar Chicago ta bai wa Atiku takardun shaidar karatun Tinubu.
A labarin, an ruwaito wata kotu a Amurka ta umarci Jami’ar Jihar Chicago ta bai wa Atiku Abubakar takardun shaidar karatun Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a cikin kwanaki biyu.
A ranar Talata ce 19 Ga Satumba ta bayar da wannan umarni.
Kotun ta Gabacin Illinois, ta umarci Jami’ar Chicago cewa ta bayar da kwafe-kwafen dukkan takardun bayanan da Atiku ya nema.
Mai Shari’a Jeffrey Gilbert na Kotun Majistare ne ya bada umarnin a ranar Talata.
Atiku ya shigar da ƙarar neman kotu ta sa jami’ar ta ba shi takardun tun a ranar 2 Ga Agusta.
Neman takardun dai na daga cikin kwatagwangwamar shari’ar zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 Ga Fabrairu, 2023, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta ce Bola Tinubu na APC ne ya yi nasara.
Atiku wanda ya zo na biyu da Peter Obi wanda ya zo na ɗaya, sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, kuma su ka garzaya kotu.
Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jaddada nasarar Tinubu, wanda hakan ya sa Atiku da Obi garzayawa Kotun Ƙoli.
Atiku ya ce ya na so Jami’ar ta ba shi kwafen takardun shaida na Tinubu na asali, domin a Najeriya kwafen shaidar biyu ne ke yawo, kuma sun sha bamban da juna.
Atiku ya ce akwai wanda ke ɗauke da ranar 27 Ga Yuni, 1979 da kuma mai ɗauke da ranar 22 ga Yuni, 1979, dukkan su dai su na ɗauke da shaidar kammala Difiloma da Tinubu ya yi.
Atiku kwafen takardun biyu sun sha bamban, baya ga bambancin rana, akwai bambancin rubutu, bambancin tambari da kuma bambancin sa hannu.
A kan haka ne ya ce don haka idan ba orijinal Tinubu ya bayar ba, to bai cancanta ya tsaya takara ba kenan.
Can a kotun Amurka kuwa, kwana ɗaya bayan ƙarar da Atiku ya shigar ta neman a ba shi kwafen takardun shaidar Tinubu, sai lauyoyin Tinubu su ka nemi kotu ta shigar da Tinubu cikin shari’ar.
Tinubu ya ce batun neman kwafen takardun shaidar na sa da Atiku ke yi bai taso ba, domin maganar ba ta cikin bayanan ƙarar da Atiku ya shigar kan rashin yarda da nasarar Tinubu a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a Najeriya.
Sai dai Atiku ya shaida wa kotun Amurka cewa ai Kotun Ƙoli za ta iya amincewa ya shigar da ƙarin hujjoji kamar yadda Dokar Zaɓen Najeriya ta 2022 ta tanadar.
Kotun Amurka ta ce ta amince da buƙatar Atiku, don haka ta umarci Jami’ar Jihar Illinois ta ba shi kwafen takardun shaidar Difiloma ɗin TInubu a cikin kwanaki biyu, domin ya tantance.
Kwafe-kwafen Takardun Da Jama’ar Illinois Na Tinubu Da Kotu Ta Ce A Gaggauta Bai Wa Atiku:
1. Ainihin kwafen satifiket na kammala Difiloma ɗin TInubu a 1979.
2. Diflomar ‘Intervenor da aka ba Tinubu a 1979.
3. A haɗa wa Atiku da kwafen shaidar kammala Difiloma na wani daban, wanda ke da irin tambari, hatimi da sa hannu irin wanda na Tinubu ke ɗauke da shi.
Discussion about this post