Sanatan Nasarawa ta Kudu, Mohammed Onawo, ya yi zargi tare da ragargaza ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, dangane da yadda ya ke gaggawar amincewa da wasu ƙudirorin da aka gabatar ba bisa ƙa’ida ba.
Ya zargi Akpabio da cewa ba ya bari sai yawan sanatocin da ke zauren majalisa sun kai kashi 2 bisa uku kafin a amince da wani ƙudiri, amma sai kawai Akpabio ya zartas da amincewar a haka.
Onawo wanda ɗan Jam’iyyar PDP ne, ya yi wannan zargi da ragargaza a lokacin da ya ke shigar da tsokacin hanzari kan buƙatar neman amincewa a yi wa Dokar Shirin Inganta Rayuwar Al’umma (NSIP) kwaskwarima, a ranar Larabar da ta gabata.
An gabatar da roƙon amincewa da ƙudirin a cire Shirin NSIP kacokan daga ƙarƙashin Ma’aikatar Agaji da Jinƙai, a maida shi ƙarƙashin Ofishin Shugaban Ƙasa.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele ne ya bijiro da roƙon ƙudirin, daga ɓangaren zartaswa na Gwamnatin Tarayya.
Shi kuwa Sanata Mohammed Onowo, ya ƙalubalanci yadda Akpabio yadda ya yi gaggawar amincewa da ƙudirorin.
“Kafin a amince da ƙudiri tilas sai an tabbatar cewa akwai sanatoci kashi 2 bisa 3 a zauren nan. To shin ko an yi la’akari da cewa yawan mu ya kai hakan ko bai kai ba?
“Sannan kuma bayan wannan, tun farkon zaman wannan majalisa a wannan zango, kai Shugaban Majalisar Dattawa ka ce wannan zangon majalisa, majalisa ce mai yin gyare-gyaren abin da aka yi ba daidai ba.
“To amma abin mamaki, a duk lokacin da aka gabatar da wata buƙata, sai yi gaggawar amincewa nan da nan a gaggauce, kamar ƙibtawar walƙiya.
“Tilas a ce kowane sanata an sanar da shi abin da ƙudirin ya ƙunsa ko kuma zai ƙunsa. Shi kuma sai ya je ya yi bincike da nazari, daga nan ya dawo zauren majalisa ya bayar da gudummawa mai muhimmanci.
“Amma a yanayi wanda hatta ƙudirin magana kan kuɗaɗe ma idan an kawo, ana so mu amince da shi cikin sa’o’i kaɗan, wannan ba alheri ba ne, rufa-rufa ce kawai kuma ba a nufin ƙasar nan da alheri.
“Yallaɓai kai ne Shugaban Majalisar Dattawa a yau, amma ranar da babu kai, tarihi zai zartas maka da hukuncin cewa irin waɗannan abubuwan da ka ke aikatawa, ba ka nufin ƙasar nan da alheri.” Haka Sanata Mohammed ya furta wa Akpabio gaba da gaba.
Shi kuwa Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, cewa ya yi kashi 2 bisa 3 da ake magana na yawan sanatoci ya nufin na waɗanda ke zaune a zauren, ba na yawan adadin sanatocin 109 da ake da su ba.
Shi kuma Akpabio ya maida masa martanin cewa, “to idan mun yi gaggawar amincewa da ƙudiri don alheri ga Najeriya, tarihi zai yi mana hukunci.
“Gaggawar amincewa da ƙudiri matsawar an yi ne kan abin da zai zama alheri ga ƙasa, to wannan ba wani abu ba ne. Kuma ba na jin mun zo nan ne don mu riƙa gudanar da abin da ba alheri ba ne ta ƙasar nan. Tsokacin da ka yi kuma na karɓa.”
Discussion about this post