Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa ba za a rabu da yawan juyin mulki a Afrika ba, har sai an ɗora dimokraɗiyya bisa kyakkyawan tsari.
Jonathan ya bayyana haka a ranar Juma’a, lokacin da ya ke jawabi wurin taron Tattauna Ƙalubalen Dimokraɗiyya a 2023, wanda Gidauniyar Inganta Dimokraɗiyya ta Goodluck Jonathan Foundation ta shirya a ranar Juma’a, a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.
Tsohon shugaban na Najeriya, ya nuna damuwar sa ganin yadda a cikin ‘yan shekarun nan yadda a nahiyar Afirka Dimokraɗiyya ke haddasa gagarumin rikici da manyan matsaloli, ciki har da haddasa fatara, talauci da yunwa da kuma rashin aikin yi.
Jonathan ya ce waɗannan da wasu musabbaban sun jawo al’umma sun daina bai wa dimokraɗiyya amanna.
“Shi fa shugabanci ya wajaba a ce ya na tabbatar da nagartacciyar dimokraɗiyya, zuwa bunƙasa tattalin arzikin al’umma.”
“Baya-bayan nan mun sha ganin yadda ‘yan ƙasa ke yawan zagwaɗi da murna har da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, idan sojoji suka kifar da mulkin dimokraɗiyya a Afrika.
“Duk da dai wannan zagwaɗi da zumuɗin ba ya ɗorewa sosai, to amma dai hakan ya na nuna cewa akwai buƙatar a sake tsari da fasalin dimokraɗiyya a Afrika.
“A matsayin mu na shugabanni, wajibi ne mu tabbatar cewa dimokraɗiyya na bai wa ‘yan ƙasa haƙƙin su da cikakken ‘yancin su. Kuma mu tabbatar mu na kawo ci gaba wanda ke yin tasiri wajen gina al’umma.” Inji Jonathan.
Discussion about this post