An bayyana cewa ‘yan bindigar da suka kwashi ɗalibai mata biyar na Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma, cikin Ƙaramar Hukumar Katsina, sun aika aika-aikar ne a matsayin ramuwar-gayya kan wani farmakin da jami’an tsaro suka kai wa iyayen su da dangin su ‘yan bindigar.
Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, Farfesa Armaya’u Bichi ne ya bayyana haka.
Ya faɗi haka a wata tattaunawa da ya yi da Sashen Hausa na DW, a ranar Juma’a.
Ya ce waɗanda suka yi garkuwa da ɗaliban ne da kan su suka bayyana haka, lokacin da ake ƙoƙarin yin sulhu da su ta wayar tarho.
An yi garkuwa da ɗaliban mata ne a ranar Laraba, lokacin da ‘yan bindiga suka dira gidan kwanan su da ke unguwar Mariamoh Ajiri, a Dutsinma.
Sai dai kuma Bichi bai ce ko masu garkuwa ɗin sun nemi a biya su kuɗin fansa ba, kafin su saki ɗaliban.
“Ana dai ci gaba da tattaunawa. Su ma jami’an tsaro a jihar na bakin ƙoƙarin su son su ceto ɗaliban.
“Yan bindigar sun yi magana, sun ce sun kwashi ɗaliban ne a matsayin ramuwar-gayyar kai wa iyayen su hari da jami’an tsaro suka kai masu a Ƙaramar Hukumar Batsari.
Rahotanni sun ce an kai wa iyayen ‘yan bindiga ɗin hari, har aka banka wa gidajen iyayen na su wuta, kuma aka kwashe masu dabbobi da kayan abinci.
“Sun so yin harin ramuwar-gayya a Batsari, amma sai wata zugar ‘yan ta’adda suka ƙi yarda a kai hari a Batsari, gogarman su ya hana shi. To shi ne sai suka kai harin kan ɗalibai mata na Jami’ar Dutsinma.” Cewar Bichi.
“Amma an shaida masu cewa mutanen Dutsinma da ɗalibai mata na Jami’ar Dutsinma ba su yi masu laifin komai ba. Don haka su sake su kawai.
“To kuma na yi amanna cewa da yardar Allah za su sake su.”
Ya ce an sha gargaɗin ɗalibai su daina kama hayar gidan zama a cikin gari, saboda su na ɗaukar hankalin masu garkuwa da mutane.
Discussion about this post