Wasu da ake zargin Ƴan ta’adda ne sun yi garkuwa da wasu dalibai mata 5 na jami’ar tarayya ta Dutsin Ma da ke jihar Katsina a safiyar ranar Laraba.
Wani ma’aikacin jami’ar ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa daliban da aka sace suna zaune ne a gida daya a unguwar Mariamoh Ajiri a cikin garin Dutsin Ma.
Da suka kai hari gidan, ‘yan ta’addan sun nausa da daliban biyar cikin dajin da ke kusa da makarantar. Na samu labarin cewa an kira ‘yan banga amma ‘yan ta’addan sun tsere kafin ‘yan banga su iso.” Inji ma’aikacin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai ba.
Ya ce dalibai kadan ne suka rage a Jami’ar domin da daman su sun koma gida bayan kammala jarabawarsu.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abubakar Sadik, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an yi garkuwa da ɗaliban. Ya ce ƴan sanda sun kama wani da ake zargi da hannu a kai wannan hari.
Zan iya tabbatar da cewa an sace dalibai biyar amma an kama wani da ake zargin yana da hanna a kai wannan hari. Mun fara bincike.
Kakakin Jami’ar, Habibu Aminu, shi ma ya tabbatar da sace daliban. Ya ce ana kokarin ceto su.
Discussion about this post