Wani riƙaƙƙun ‘yan bindiga sun tare hanya da rana, kafin Sallar La’asar har suka sauke lodin matafiya su 25, su ka darzaza da su a cikin daji.
Mummunan lamarin ya faru ranar Juma’a, inda matafiyan da aka yi garkuwar da su mawaƙan begen Yesu Almasihu ne a Cocin Christ Apostolic da ke Oke Igan, Akure a Jihar Ondo.
Mahara sun tare motar da su ke ciki, suka sauke lodin su a kan babbar hanya ta Akure zuwa Benin, wadda ba ta rabo da zirga-zirgar motoci.
Sun tare matafiyan a kusa da garin Elegbeka, lokacin da su ke kan hanyar zuwa taron jana’iza a garin Ifon a Ƙaramar Haukumar Ose a Jihar Ondo ɗin.
Su na kan hanyar tafiya ne wurin rufe gawar babban mai shirya masu waƙoƙin bege, wanda ya rasu.
‘Yan bindiga sun tare motar da su ke ciki wajen ƙarfe uku na yamma, a jiya Juma’a.
Hanyar duk da babba ce mai hannu huɗu, ta yi ƙaurin su na wajen matsalar yadda ‘yan bindiga ke tare matafiya, su na yin garkuwa da su.
Matafiya kan yi rashin sa’a inda maharan kan tsaya daidai wuraren da titi ya lalace, inda tilas sai direba ya taka burki ya tafi a hankali, kamar zai shiga ɗaki.
“Waɗanda aka yi garkuwar da su duk coci ɗaya muke da su, wato cocin CAC na Oke-gan, Akure.” Haka wani ɗan cocin su ya shaida wa manema labarai, yau Asabar a Akure.
Ya ce ‘yan bindiga ɗauke da zabga-zabgan bindigogi sun tasa ƙeyar matafiyan sun nausa da su cikin daji. Kuma shiru ka ke ji har yanzu, ba amo ba labari.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Ondo, Funmilayo ta tabbatar da faruwar kama matafiyan.
“Amma an ceto wasu, kuma yanzu haka ‘yan sanda na ƙoƙarin ceto ragowar.
Discussion about this post