Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda a ranar Talata ya kaddamar da kungiyar tsaro domin yakan rashin tsaro a jihar.
A taron kaddamar da rukunin farko na jami’an tsaron da aka yi a jihar Radda ya ce gwamnati ta yi haka ne domin hada hannu da mutane domin kawar da hare-haren‘yan bindiga a jihar.
Bisa ga takardar da kakakin gwamnan Ibrahim Kaula ya fitar ya ce mutum 2,400 ne ke cikin rukunin farko da aka kaddamar kuma an zabo su ne daga kananan hukumomi 34 dake Katsina.
Gwamnan ya ce kafin ya zama gwamnan jihar ya ziyarci kauyuka 361 dake jihar inda ya ga yadda kauyukan ke fama da rashin tsaro.
Ya ce akalla kananan hukumomi 22 daga cikin 34 din da ake da su a jihar na fama da hare-haren‘yan bindiga.
Radda ya ce ya kafa kungiyar jami’an tsaron ne bisa ga shawarar kwamitin da ya kafa domin samar da mafita kan matsalar rashin tsaro a jihar.
Ya yi kira ga zaratan dakarun su kwatanta gaskiya da adalci a aikinsu tare da zama abin koyin ga mutane a jihar.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu, gwamnan jihar Kebbi Nasir idris, gwamnan jihar Kano Abba Kabir, gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni da gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron kaddamarwar.
Discussion about this post