Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta bayyana cewa fitaccen mawaƙin nan Azeez Fashola da aka fi sani da Naira Marley, ya na hannun su.
Haka dai wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Legas, David Hundayin ya fitar ta ƙunsa.
Shi ma Naira Marley ɗin ya bayyana cewa ya kai kan sa ga hukumar ‘yan sandan Legas, jim kaɗan bayan dawowar sa daga Ingila, don ya taimaka wajen binciken gano musabbabin rasuwar mawaƙi Mohbad.
“Na sadaukar da kai na domin na tabbatar da ba ni da hannu a mutuwar Mohbad, kuma ina bada haɗin kai ga hukuma domin na tabbatar da cewa gaskiya ta ta wanke ni daga zarge-zargen da wasu ke yi min.”
Ya kuma ƙaryata zargin da ake yi masa cewa ya kafa guruf ɗin kamfanin sa na Marlian Record a matsayin hanyar safarar muggan ƙwayoyi.
Naira Marley ya ce ya lura tun bayan rasuwar Mohbad ya ake ta yaɗa maganganu na ɓata masa suna. Ya ce kowa ya san shi ya na London ma Mohbad ya rasu, kuma ya dawo ne domin ya taya ‘yan sanda binciken gano musabbabin mutuwar Mohbad.
Tun bayan mutuwar Mohbad da tono gawar sa da aka yi domin bincike, jama’a sun riƙa jefa zargi kan Sam Larry da Naira Marley.
Tuni dai kwanaki uku baya kenan Sam Larry ya Miƙa kan sa ga ‘yan sanda.
Discussion about this post