Balarabe Abbas, wanda aka maye sunan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sunan sa a matsayin Minista daga Kaduna, ya yanke jiki ya faɗi wurin da tantance shi a Majalisar Dattawa.
An dakatar da tantance El-Rufai a cikin watan Agusta, lamarin da ya haifar da maganganun da har yau ba a daina watsawa ba.
Balarabe Abbas ya faɗi a yau Laraba a daidai lokacin da ya ke bayyana irin nasarorin da ya cimma a rayuwa a harkokin kan sa da kuma a aikin gwamnati.
Lamarin ya faru wajen ƙarfe 1:50 na rana, inda faɗuwar sa ke da wuya sai Sanatoci suka yi kan sa a guje, domin su ceci rayuwar sa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya riƙa kururuwar a kawo agajin ruwa da kuma sukari.
Abbas shi ne mutum na biyu a jerin tantancewar da za a yi wa ministocin uku.
Tuni dai Akpabio ya ce Majalisa za ta yi zaman sirri, ba tare da manema labarai da ‘yan kallo ba.
Discussion about this post