Wata kotun yanki da ke Centre-Igboro, Ilorin a ranar Juma’a, ta raba auren Majeed Suleiman da Ganiyat Suleiman bisa bukatar miji, saboda zargin zina da ya ke yi wa matar ta sa.
Alkalin kotun, AbdulKadir Ahmed, ya ce bayan sauraron bangarorin biyu, kotun ta lura da cewa akwai takaici a halin da mai karar ke ciki yayin da wanda ake kara ta nuna halin rashin gaskiya da ko a jikinta.
Alkali Ahmed ya ce, “sakin aure ba abu ne da za a yi gaggawar yanke hukunci ba, amma a yanayin da mai shigar da kara ya dage ya yi kamar ba zai iya jure wa abokin zamansa ba, sai a duba yiwuwar saki a yi shi kawai.”
Da haka ne alkali ya raba auren da aka yi tsakanin mai kara da wanda ake kara, sannan ya umurci wanda ake kara da ta yi iddarta wata uku a gidanta na aure.
Tun da farko dai wanda ya shigar da kara ya shaida wa kotun cewa matarsa ta shafe shekaru bakwai tana yin zina, inda ya kara da cewa ba zai iya jurewa da ita ba.
“Na zo kotu ne kawai saboda ba na son in dauki doka a hannuna ko kuma in yi mata tilis a gidana sannan in fatattake ta, shi ya sa na zo kotu kawai don ayi abinda ya dace
” Ba zan iya cigaba da zama da wannan mata ba. Ga shi kuma ‘ya’yan mu sun girma kuma ace wai tana zinace-zinace a titi.
Sai dai kuma ita Ganiyat ta roki kotu ta barta ta cigaba da zama a gidan tsohon mijinta saboda ta rika gani da kula da ‘ya’yan ta.
Discussion about this post