Jam’iyyar APC ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ne ke rike da sarautar wanda ya fi kowa takarar shugaban kasa ana kuma zabga shi da kasa a Najeriya, kuma duk da haka bai dandara ba.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC Felix Morka, a wata doguwar martani da jam’iyyar ta fitar kan jawabin da Atiku ya yi a wurin ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Moka ya ce da dai Atiku zai gane, da ya ja bakin sa ya yi shiru, ya daina lallafta wa in Najeriya karya na babu gaira babu dalili.
” Gashi saboda rudewa da neman mulki ko ta halin kaka, har Amurka ya garza ya yanan neman yadda za a yi ya samu wani abu da zai sa dole sai ya zama shugaban kasa. Ya tafi can neman lakani, da siddabarun da za su sa ya zama shugaban kasa tunda a zabe an yi wujiwuji da shi.
“A yayin da muke jajanta wa Alhaji Atiku Abubakar bisa yadda ya shafe tsawon rayuwarsa yana hakon neman abinda da bai tabbata masa ba har yanzu, Muna ja masa kunne cewa ya na kuma neman ya wuce gona da iri, domin abinda yake yi cin fuska ne ga ofishin shugaban kasar Najeriya a idon duniya.
“A haka muna so mu yi karin haske kan ainihin abinda ya faru a Amurka wajen mika takardun kammala karatun shugaba Tinubu da magatakardar Jami’ar jihar Chicago CSU ya bada domin ‘yan Najeriya su fahimci abinda ya faru, su daina biye wa labaran kanzon kuregen da Atiku da makarraban sa suke shafa musu domin wata manufa ta su can.
Abinda Westberg ya fadi a kotun Amurka Kan takardun Tinubu
1 – Bola Ahmed Tinubun da ake fadi ya yi jami’ar Chicago, shine dai Tinubun da a ke ceckuce akai. Ba wani bane .
2 – Ya tabbatar da cewa wani mai suna Adeniji da ya fito ya ce ajinsu daya da Tinubu, da gaske dalibi ne a CSU kuma a lokaci guda su biyun sun fito neman mukaman kungiyar dalibai na jami’ar.
3 – Sannan kuma wannan shaidar satifiket na Difloma da Atiku ke ta korafi a kai, ba shaidar Karatu bace sahidar karramawa ce wanda aka bashi a jami’ar kuma ana yin irin haka a kowace jami’a a Amurka. Ba sabon abu bane.
4 – Bayan haka ya ce makarantar Southwest da Tinubu ya yi wacce da ita ce ya samu shiga Jami’ar CSU, babu matsala a suna ko takardun da ya yi amfani da su. Bola Tinubu ne dai wanda ake magana, kuma shine dai ya shiga jami’ar CSU. Saboda haka wannan dai da ya kammala karatu a Kolejin Southwest, shine ya yi jami’ar CSU, wato shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na Najeriya yanzu.
Sannan kuma muna so mu sanar wa ‘yan Najeriya cewa babu wani wuri da Magatakarda Westberg ya fadi a kotun Amurka cewa wai Tinubu ya mika shaidar karatu na boge ga hukumar Zabe (INEC). Hakan wani makirci ne na Atiku don ya kawo rudani a zukatan ‘yan Najeriya.
Abun da ya kamata a sani shine, Tinubu da kan sa ya shiga wannan jami’a, ya yi karatu a can sannan kuma ba karatu ba kawai yana daga cikin dalibai masu hazaka, kuma fitattu a lokaci, sai kuma da kan sa ya buga abinda ya yi na boge ya mika wa wani ko wasu. Ina hankali zai dauki haka idan ba neman magana irin na Atiku da ‘yan adawa ba.
Discussion about this post