Majalisar dattawa a ranar Laraba ta tabbatar da nadin Balarabe Lawal (Kaduna), Ayodele Olawande (Ondo) da Jamila Bio Ibrahim (Kwara) a matsayin ministoci.
Tabbacin da majalisa ta yi a yau Laraba ya kawo adadin ministocin da za su yi aiki a gwamnatin shugaba Bola Tinubu zuwa 48.
Ibrahim da Olawande za su rike ma’aikatan matasa ne.
Shi kuwa Balarabe Lawal zai rike ma’aikatar Muhalli.
Discussion about this post