Kotun Musamman ta Sojojin Najeriya ta ɗaure Manjo Janar Umaru Mohammed tsawon shekaru bakwai a kurkuku.
Kotun wadda ta yanke hukuncin a ranar Talata, ta kuma umarci da tilas ya amayo dala miliyan 2.1 da kuma naira bilyan 1.06, Kuɗaɗen da ya sace.
Yayin da ya ke karanto hukuncin, Shugaban Kotu Manjo Janar James Myam, ya ce an samu Janar Umaru da laifuka 14 daga cikin tuhuma 18 da aka yi masa.
Myam ya ce ya ɗaure Umaru bisa tsarin Dokar Aikata Laifuka ta C38, ta Tarayyar Najeriya, ta 2004, sai uma Sashe na 174 na Dokar Sojoji, ta 20 kuma ta 2004.
Myam ya ce kotsu ta yi masa sassauci saboda bai wahalar da shari’a ba. Sannan kuma idan bai gamsu ba, zai iya ɗaukaka ƙara.
Ya aikata laifukan ne a lokacin da ya ke Shugaban Hukumar Kula da Kadarorin Hukumar Sojojin Najeriya.
Kotun Sojoji ta ɗaure Janar Mohammed Umaru shekaru bakwai, ta ce ya biya naira biliyan 3 da ya sace.
Kotun Musamman ta Sojojin Najeriya ta ɗaure Manjo Janar Umaru Mohammed tsawon shekaru bakwai a kurkuku.
Kotun wadda ta yanke hukuncin a ranar Talata, ta kuma umarci da tilas ya amayo dala miliyan 2.1 da kuma naira bilyan 1.06, Kuɗaɗen da ya sace.
Yayin da ya ke karanto hukuncin, Shugaban Kotu Manjo Janar James Myam, ya ce an samu Janar Umaru da laifuka 14 daga cikin tuhuma 18 da aka yi masa.
Myam ya ce ya ɗaure Umaru bisa tsarin Dokar Aikata Laifuka ta C38, ta Tarayyar Najeriya, ta 2004, sai uma Sashe na 174 na Dokar Sojoji, ta 20 kuma ta 2004.
Discussion about this post