Jami’ar CSU ta birnin Chicago a Amurka, ta tabbatar da cewa Shugaban Najeriya Bola Tinubu tsohon ɗalibin ta ne, kuma ya kammala jami’ar tabbas.
Hakan na ƙunshe cikin takardun bayanan zaman da Tinubu ya yi a jami’ar, wanda ta damƙa wa lauyoyin Atiku Abubakar a ranar Litinin, bisa umarnin Kotun Gundumar Arewacin Illinois.
A ranar Talata, 3 ga Oktoba kuma, sai Rajistara na jami’ar, Caleb Westberg ya gabatar wa kotun dukkan kwafen bayanan da ta ce a bai wa Atiku Abubakar, abokin takarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu.
PREMIUM TIMES ta samu dafe kwafe-kwafen dukkan bayanan da kotun ta fitar.
Kallo Ya Koma Amurka:
Yadda Lauyoyin Atiku Suka Shafe Sa’a Ɗaya Cur Su Na Yi Wa Rajistaran Jami’ar Chicago Tambayoyi A Gaban Mai Shari’a:
A cikin kwafe-kwafen hayanan da PREMIUM TIMES ta samu, har da kwafen dukkan tambayoyin da lauyoyin Atiku suka riƙa sheƙa wa Rajistaran CSU.
Tun farko dai a nan Najeriya Atiku ya nuna tababar sahihancin Satifiket ɗin da Tinubu ya damƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, shi da lauyoyin sa su na iƙirarin cewa na bogi ne.
A kan haka ne su ka ce tunda har Tinubu ya tafka laifin gabatar wa INEC da katin shaidar kammala Difiloma/Digiri na Jabu, to bai cancanta ma ya tsaya takara ba.
Sai dai kuma Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa ta kori ƙarar da Atiku ya shigar, inda ta ce Atiku ya kasa kawo hujja.
Wannan ɓacin rai ne ya sa Atiku ya shigar da ɗaukaka ƙara a Kotun Ƙoli, inda a yanzu ya ke so zai gabatar da takardun jabun da kotun baya ta ce babu hujja.
Karankatakaliyar Da Ke Cikin Bayanan Da Kotun Amurka Ta Bai Wa Atiku Kan Tinubu:
Dama an riƙa yaɗa ji-ta-ji-tar cewa da sakamakon jarabawar wani ko wata Tinubu ya shiga Jami’ar Chicago, CSU.
Ya shiga jami’ar da sunan wata mata wai ita Bola A. Tinubu. Domin a satifiket ɗin, alamar ‘F’ aka rubuta daga sakandaren da Tinubu ya ce ya fita, wato mace kenan.
Bayanan da Rajistaran CSU ya yi sun ƙunshi shafuka 125. A cikin an tabbatar da cewa Tinubu ya halarci CSU daga Agusta 1977 zuwa Yuni, 1979.
“An damƙa masa Digiri kan Tsarin Kasuwsnci, wato BSc. Business Administration, a cikin Yuni, 1979.
Rajistara ɗin ya kuma tabbatar cewa Tinubun dai shi ne wannan da a yanzu ya ke shugaban Najeriya.
Lauyoyin Atiku sun tambaye shi ko ya taɓa ganin Tinubu ido-da-ido? Kuma ko ya taɓa kai ziyara jami’ar, ko kuma idan ya taɓa bayar da gudummawar kuɗaɗe ga jami’ar. Rajistara ya duk ya ce a’a.
Discussion about this post