Jami’ar Jihar Chicago (CSU) mika bayanan karatun Shugaba Bola Tinubu ga abokin hamayyarsa Atiku Abubakar, bisa umarnin wata kotu a Amurka.
Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen Najeriya na 25 ga Faburairu, ya bukaci takardun da za su tabbatar da zargin da ya ke yi wa shugaba Tinubu cewa takardun kammala karatunsa na jami’ar CSU jabu ne. Hakan na nufin Tinubu bai cancanci tsayawa takara ba kenan idan ya tabbatar da haka a kotu, kuma ya yi nasara a kan haka.
A ranar Litinin jami’ar ta mika wa lauyoyin Atiku, tarin takardu da ke da alaka da karatun Tinubu a jami’ar ta CSU.
Takardun sun kunshi bayanan karatun sa da takardun kammala karatun sa a jami’ar da na shiga da sauran su.
Yanzu dai abu ya rage wa kotu su duba su bayyana wa ƴan Najeriya ina aka dosa.
Discussion about this post