Kungiyar Hamas masu fafutukar kafa kasar Isra’ila sun yi gargaɗin cewa lallai idan Isra’la bata kyale motocin abinci na tallafi na shiga Falasɗinu ba, ba za ta sake sakin ɗan Isra’ila da suka yi garkuwa da su ba.
A ranar Litinin ƙungiyar Hamas ta saki wasu mata biyu ƴan Isra’ila da ke tsare hannunsu daga zirin Gaza. Sannan kuma An sako wasu ‘yan kasar Amurka biyu a ranar Juma’a.
Sama da mutane 220 ne ake garkuwa da su baki daya.
Saboda dalilai na jin kai, mun saki mutum hudu (wadanda ke tsare hannun mu) ba tare da wani sharadi ba,” Osama Hamdan.
” Amma fa sai dai a sani cewa daga yanzu sai an tilasta wa Isra’ila su riƙa bari motocin agaji na shiga Gaza daga kasar Masar, wato daga iyakar Rafa, ana kai wa Falasɗinawa man fetur, ruwa, magani da abinci. Wannan shine sharaɗin mu daga yanzu kafin mu sake sakin wani da ke tsare hannunmu.
Muna bukatar Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa mutanenmu domin mu samu damar sako mutanen da aka kama,” inji Hamdan.
Akalla Isra’ilawa 222 ne ke tare hannu Hamas. Sannan har yanzu ana ci gaba da yi wa mutanan Gaza luguden bamabamai babu ƙaƙautawa.
Discussion about this post