Ofishin Kula da Ayyukan Jinƙai da Agajin Gaggawa na Majalisar Ɗinkin (OCHA), ya ce matsalar ayyukan jinƙai da agaji ta yi muni sosai a yankin Gaza da ke ƙarƙashin Falasɗinu.
Hukumar Agajin wadda ita ce mafi girma yanzu a Gaza mai bayar da agaji da jinƙai, ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar ita ma tilas ta dakatar da gudanar da ayyukan ta, idan dai ba a bari an shiga da fetur ya wadata a yankin Gaza ba.
An rufe asibitoci, yayin da ba ake fama da matsalar ruwan sha da na amfanin yau da kullum, haka akwai rashin magunguna, likitoci da jami’an kula da marasa lafiya.
Ɗan fetur ɗin da ake samu ana raba shi ne kaɗan-kaɗan ga wuraren da tilas sai an raba ɗin.
Hukumar agajin ta ce yawancin janareton da ake amfani da shi a Gaza, ba a ƙera su don juriyar daɗewa su na aiki ba, ba dare ba rana ba.
Jami’an UN da suka ziyarci wasu asibitocin, sun samu ɗaruruwan maza da mata da ƙananan yara, waɗanda aka ji wa ciwo.
Da yawa daga cikin su ba su san halin da suke ciki ba, wasu na fama da raunukan da ko bandeji ba a ɗaura an rufe masu raunukan ba. Wasu ma a ƙasa kan daɓen siminti su ke kwakkwance, babu jami’an lafiyar da za su kula da su.
A farfajiyar asibitin akwai tanti wanda cike ya ke da gawarwaki har da na ƙananan yara.
Hukumar Agajin ta UN ta ce an ajiye gawarwakin a cikin tanti, saboda ɗakunan ajiye gawarwakin asibitin duk cike su ke.
Haka kuma akwai ƙarancin abinci, yayin da rumbunan ajiye kayan abinci sun zama ƙarƙaf.
Hukumar Abinci ta Duniya ta ce abincin da ke yankin Gaza a yanzu zai iya ƙarewa ƙarƙaf, nan da kwanaki 12.
Amma kuma kayan masarufi da ke cikin kantina ba za su iya wuce kwanaki biyar kafin su ƙare ba.
Mutane da yawa sun koma shan ruwan rijiya, wanda ke da zartsin gishiri sosai, kuma ya na da barazana ga lafiyar jama’a.
Jami’an lafiya sun gano ɓarkewar ciwon ƙyanda, ƙazuwa, da kuma amai da gudawa, sakamakon rashin tsaftar muhalli da rashin ruwan sha mai tsafta.
An ƙiyasta cewa akwai sama da mutum miliyan 1.4 da suka rasa muhallin su, yayin da daga cikin adadin, mutum 590,000 su na zaune ne a sansanin gudun hijira ma Majalisar Ɗinkin Duniya.
Fiye da kashi 15 bisa 100 na waɗanda suka rasa muhallin su na fama da naƙasa, sannan kuma matsugunan da suke ciki babu abubuwan buƙatu na dole, na yau da kullum. Kamar yadda rahoton ya nuna.
Mahukuntan yankin Gaza sun ce an lalata kusan kashi 40 bisa 100 na rukunin gidajen yankin Gaza, inji Hukumar Agajin Gaggawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya, OCHA.
Chana Ta Bijere Wa Matsayar Amurka Kan Yaƙin Isra’ila Da Falasɗinu:
“Mun yi tir kuma ba mu yarda da ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula ba. Kuma muna kira a bi hanyar diflomasiyya domin a saki waɗanda ake tsare da su.
“Ba mu yarda da ƙudirin da bai nuna a daina yin amfani da sojoji ana kai hare-hare ba. Kuma duk ƙudirin da Amurka ta ɗauka wanda bai yarda a yi binciken wannan mummunar ɓarna ba, to mu ma ba mu yarda da ƙudirin na ta a Majalisar Ɗinkin Duniya ba.
“Hare-hare irin wanda aka kai a Asibitin Al-Ahli, muddin ba a bincike shi ba, to akwai munsficci, saboda ya kashe fararen hula da dama.”
Haka Wakilin Chana na Dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Zhang ya bayyana a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ya ce su a koda yaushe su na so a tsagaita wuta, a bada dama kayan agajin gaggawa su isa wurare, domin kaucewa wa bala’in da ka iya afkuwa nan gaba.
“Ba mu yarda da matsayar da Amurka ta cusa a majalisa ba, domin ba a dubi ainihin musabbabin rikicin Isara’ila da Falasɗinu a Gaza ba.
“Saboda ƙudirin bai umarci Isra’ila ta janye mamayar da ta yi wa yankin Gaza ba, kuma ta janye umarnin ficewar Falsɗinawa daga Arewacin Gaza.”
Discussion about this post