Gwamna Dauda Lawal na Jihar, ya fallasa wata badaƙala da tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi kan ginin filin jirgin sama na Zamfara.
Gwamnan ya zargi tsohuwar gwamnatin da fidda kuɗi har Naira biliyan 6,775,949,561.50, don samar da tashar jirgin sama wanda tuni aka watsar da aikin.
Wata takardar sanarwar manema labarai wacce Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Alhamis, a Gusau, ta ce gwamnatin Zamfara ta shiga cikin alhini yayin da ta bankaɗo irin ɓarnar da gwamnatin da ta gabata ta aikata kan aikin filin jirgin sama.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin Dauda Lawal ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wurin bincike tare da fallasa duk wata ɓarna domin ganin maɓarnata sun fuskanci hukunci.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Bayan shigar sa ofis, Gwamna Lawal, a ƙoƙarin sa na tantance nisan da aka yi a aikin tashar jirgin sama ne ya samar da kwamitin mutum biyar domin su yi aikin binciken halin da aikin ke ciki.
“Kwamitin a rahotan sa ya bayyana cewa kamfanin Avic International Engineering Limited ne ya bayar da taswirar tashar jirgin. Kuma wannan ɗan kwangila ne ya yi gaban kan sa wurin bayar da jadawalin aiki ba tare da sa hannun hukumomin gwamnati da suke aikin tantancewa da tabbatar da ƙa’ida ba.
“An ba wannan kamfani na Avic International Engineering Limited kwangilar aikin ne a ranar 15 ga Mayu 2019, kamar yadda yake a takarda mai lamba FGPC/SEC/NOT/2019/055. Kan kuɗi Naira Biliyan 11,551,899,123.00.
“Kwamitin ya fallasa cewa ba a samo umurni daga hukumomin Gwamnatin Tarayya ba kafin ma a bayar da aikin. Wani kamfani mai zaman kan sa, BJ Aerotronic shi ne aka ɗauka domin samo wannan umurnin aikin bayan an ma fara aikin. An biya ‘yan kwangilar kuɗi ba tare da bin duk wata ƙa’ida da doka ta tanada ba.
“A saboda haka ne kwamitin ya bayyana irin badaƙalar da ke cikin aikin tun daga tushen sa.
“An biya ‘yan kwangilar kaso 30% na aikin a matsayin biyan farko, inda aka ba su Naira Biliyan 3,465,569,736.90 daga asusun Ma’aikatar Kuɗi ta jiha a ranar 19 ga Yuni, 2020. A matsayin biya na biyu, an sake tura musu Naira biliyan 2, 310, 379, 824.60 daga asusun Ma’aikatar kuɗin jiha a ranar 19 ga watan Yuni da sunan bashi (wanda babu wannan tsarin sam a ƙa’idar gudanarwa ta gwamnati). An sake tura musu Naira miliyan 825, 000, 000.00 daga asusun Ma’aikatar Ƙananan hukumomi a ranar 25 ga Oktoba, 2021 a matsayin biya na uku.
“Jimillar kuɗaɗen da aka tura wa waɗannan ‘yan kwangila shi ne Naira biliyan 6, 600, 989, 561.50. Wanda daga baya an biya hukumar NCAA Naira miliyan 125,000,000.00 ranar 31 ga watan Janairun 2022; sannan kuma an biya kamfanin BJ Aerotronic Limited Naira miliyan 50,000,000.00 a ranar 31 ga watan Janairun 2022, a matsayin kuɗin aikin shiga tsakani.
“Gwamnatin tsohon gwamna Bello Matawalle ta fitar da Naira bliyan 6,775,949,561.50 kan wannan filin jirgin sama.
“Sai dai, bayan da gwamnatin mu ta ɗauki kamfanoni mabambanta huɗu masu zaman kan su don yin binciken kuɗaɗen da aka kashe kan wannan aiki da aka watsar, sun bayyana cewa abin da ke ƙasa a yanzu ƙimar sa ta kai na Naira biliyan 2,249,636,040.73, wanda ana iya cewa kaso 19.47% na gabaɗaya kuɗaɗen da aka fitar.
“Haka nan kuma binciken ya fallasa cewa aikin da ke ƙasa a wurin ya saɓa da ƙa’idar da aka yi da ‘yan kwangilar⅝. Tuni ma dai ‘yan kwangilar sun watsar da aikin sun kwashe kayan su daga wurin, wanda hakan ke nuni da manufar su tun farko.
“Binciken waɗannan kamfanoni huɗu masu zaman kan su ya bayyana cewa wannan ɗan kwangila zai dawo wa da Gwamnatin Jihar Zamfara Naira biliyan 4,526,313,520.77.
“Haƙƙi ne a wuyan mu, mu ci gaba da bibiyan ayyukan rashin gaskiya tare da tabbatar da mun dawowa da al’ummar Jihar Zamfara haƙƙoƙin su da ake sace, tare kuma da hukunta waɗanda suka aikata hakan.” Cewar Gwamna Lawal.
Discussion about this post