Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ya buɗe MIQRA, Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur’ani Mai Girma. An buɗe cibiyar ce a gidan tsohon Gwamnan Kano, kuma madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Kwankwaso.
A wani shiri daga cikin shirye-shiryen taya tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso murnar cikar sa shekaru 67, Gwamna Abba Yusuf ya buɗe ya buɗe Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur’ani, wadda aka raɗa wa suna Majidaɗi Institute for Qur’anic Research and Advancement (MIQRA).
An sadaukar da cibiyar ne ga mahaifin Kwankwaso, Musa Sale Kwankwaso. Kuma an gina cibiyar a gidan Kwankwaso da ke kan titin Miller Road, Kano.
Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan Kano, Sanusi Bature ya fitar, ya ce, “da ya ke jawabi a wurin buɗe cibiyar, Gwamna Abba ya yaba wa Sanata Rabi’u Kwankwaso dangane da wannan gagarimin tanadi da ya yi wa al’umma wajen bunƙasa ilmin addinin Musulunci.”
Abba ya ce an kafa cibiyar a daidai lokacin da ya dace, idan aka yi la’akari da yawan makarantun allo da na Islamiyya da ke faɗin jihar, waɗanda ke buƙatar a narkar da su cikin tsarin makarantun zamani, domin daƙile yadda almajirai ke ta gararamba kan titina.
Gwamnan na Kano ya ƙara da cewa Sanata Kwankwaso samu gagarimar nasarar ayyukan inganta rayuwar al’umma a lokacin mulkin sa, musamman wajen bunƙasa addinin Musulunci.
Ya bada misali da aikin katange dukkan maƙabartun cikin birnin Kano, gyaran masallatan Juma’a a faɗin jiha, gina makarantun Islamiyya a ƙananan hukumomi 44.
Sai dai kuma Abba ya nuna damuwa dangane da yadda Gwamnatin da ta shuɗe a Kano, ta ƙi ƙarasa sauran makarantun da Kwankwaso bai kammala ginawa kafin cikar wa’adin mulkin sa ba.
Saboda haka sai Abba ya yi alƙawarin ƙarasa makarantun, kuma ya bada umarni ga Ma’aikatar Ilmi ta fara tsare-tsaren fara ɗaukar ɗalibai domin fara zangon karatu.
Sanata Kwankwaso ya ce an kafa MIQRA domin ta riƙa horas da mahaddata Alƙur’ani maza da mata domin samun satifiket ɗin firamare da sakandare, ta yadda za su samu hanyar zarcewa makarantun gaba da sakandare da jami’o’i.
Ɗalibai daban-daban sun jinjina wa Kwankwaso da Gwamnan Kano dangane da wannan shiri mai albarka da aka gina.
Discussion about this post