Jirgin ruwa mai ɗauke da mutum 50 ya kife a Yauri, cikin Jihar Kebbi, inda aka ceto rayukan mutum 10, sauran fasinjoji 40 kuma sun nutse a ruwa.
Jirgin ya kife da su a ranar Litinin da rana tsaka, yayin su ke tafiya da nufin zuwa cin kasuwar Yawuri.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa jirgin ya taso ne daga garin Kasabo da ke cikin Ƙaramar Hukumar Agura a Jihar Neja, zai kai ‘yan kasuwa a Yauri.
Jihohin Neja da Kebbi sun haɗa kan iyakoki a ƙananan hukumomi takwas.
Jirgin ya kife ne saboda ƙarfin igiyar ruwa a Kogin Neja, kamar yadda Shugaban Ƙaramar Hukumar Yauri, Bala Mohammed ya shaida wa Radio Nigeria a Birnin Kebbi.
Ya ce daga cikin fasinjoji 50, an samu ceto rayukan 10 kaɗai.
Sai dai kuma ya ce masu aikin ceto ba su haƙura ba, domin har yanzu su na can su na laluben sauran a cikin kogin.
Amma Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, wato NSEMA, ta ce jirgin na ɗauke ne da mutum 22 kaɗai, kuma ba a ceto ko da mutum ɗaya daga cikin su ba.
Daraktan NSEMA mai suna Salihu Garba, ya shaida wa manema labarai a Minna, babban birnin Jihar Neja cewa gwanayen nitso cikin ruwa daga ƙauyukan yankin tare da jami’an ceto na can su na bakin ƙoƙarin lalubo sauran.
Ko a makonnin da suka gabata sai da wani jirgin ya kife da mutum 26 a Jihar Neja. A Adamawa ma a wancan makon ruwa ya ci matafiya 15.
Discussion about this post