Bayanai sun ɓulla kan dalilan da su ka sa Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) da ta TUC su ka janye shirin su na shiga yajin aikin da a da za su fara a yau Talata.
Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin biyu a wani taro da ya gudana a tsakanin su jiya Litinin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Wasu daga cikin muhimman abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar sun haɗa da alƙawarin da gwamnati ta yi na ƙarin N35,000 ga duk ma’aikata har na tsawon watanni shida daga watan Satumba.
Haka kuma akwai “kafa wani kwamiti mai ƙarfi cikin wata ɗaya wanda zai duba batun ƙarin albashi ga ma’aikatan ƙasar nan.
“Janye harajin da aka sanya a harkar man gas (diesel) na tsawon watanni shida daga watan Oktobar 2023.
“Sanya naira biliyan 100 don sayo manyan motocin bas-bas masu amfani da man gas don sauƙaƙa wa jama’a hanyar zirga-zirga a duk faɗin ƙasar nan, wanda ake sa ran za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.
Haka kuma an cimma yarjejeniyar cire haraji ga wasu kamfanoni da ɗaiɗaikun jama’a don sauƙaƙa masu wajen hada-hadar yau da kullum.
Haka kuma an cimma yarjejeniyar sasantawa a ƙungiyar direbobi ta ƙasa (NURTW) tare da sanya baki a batun soke ƙungiyar masu motocin N25,000 a duk wata daga Oktoba ɗin nan ga ‘yan Nijeriya mutum miliyan15, wanda ya haɗa da tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho.
Akwai kuma ƙara faɗaɗa shirin nan na rabon taki ga manoma a duk faɗin ƙasar.
An kumma amince da cewa su ma jihohi da ƙananan hukumomi za a ƙarfafa masu gwiwa domin aiwatar da wannan ƙarin albashi ga ma’aikatan su.
Za a samar da kuɗaɗe ga matsaƙaita da ƙananan masana’antu, sannan za a mayar da hankali wajen ƙirƙiro da ayyuka ga matasa.
Za kuma a fito da shirin zagaya matatun man fetur ɗin ƙasar nan don tantance irin gyaran da su ke buƙata.
Gwamnatin Tarayya za ta yi amfani da takardun da kotu ta sahale ne wajen saka hannu a kan wannan yarjejeniyar fahimtar juna cikin mako ɗaya.
Ita dai wannan yarjejeniya ta samu sanya hannun shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, shugaba da Sakatare na TUC, Festus Osifo da Nuhu A.
A ɓangaren gwamnati kuwa akwai Ministan Ƙwadago, Simon Baƙo Lalong, da Ƙaramin Ministan sa, Nkeiruka Onyejeocha, da kuma Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris.
Discussion about this post