Kungiyar kwadago (NLC) ta dakatar da shirinta na fara yajin aikin a fadin Najeriya a yau Talata domin matsawa gwamnati kan ta magance wahalhalun mutanen kasa suka tsunduma ciki dalilin cire tallafin man fetur.
Tun bayan cire tallafin, farashin man fetur da ake siyar da shi kan kasa da Naira 200 kowace lita ya haura zuwa sama da Naira 600. Hakan ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki da abinci da sauran bubuwan bukatu da ayyuka da miliyoyin ƴan Najeriya suka dogara da su.
Kungiyar ta dakatar matakin da ta dauka na fara yajin daga ranar Talata a wata yarjejeniyar fahimtar juna da wakilan kungiyoyin kwadago da na gwamnatin tarayya suka sanya wa hannu a cikin daren jiya Litinin.
Bisa wannan yarjejeniya NLC ta dakatar da yajin aiki, sannan ta ba gwamnatin tarayya kwanaki 30, domin a cigaba da tattaunawa a tsakanin su da kuma tabbatar da ganin gwamnati ta cika alƙawuran da ta ɗauka kamar yadda suke a takardar MoU din da duka ɓangarorin suka saka wa hannun a zaman.
Cikin abubuwan da bangarorin biyu suka amince sun haɗa da biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya naira 35,000 duk wata na tsawon watanni shida masu zuwa.
Za a kaddamar da kwamitin tsara mafi karancin albashi wa ma’aikatan kasar nan cikin wata daya daga ranar da a ka kulla wannan yarjejeniya.
Sannan kuma baya ga samar da manyan motocin ɗaukan fasinja da kuma janye harajin VAT a man Dizal na wata shida, yarjejeniyar ta amince da sake duba albashin ma’aikatan manyan makarantun kasar nan domin inganta shi da kuma biyan malaman jami’o’i kuɗaɗen da suke bin gwamnati.
Bayan haka NLC ta yi kira ga gwamnatocin jihohi su yi irin haka wa ma’aikatun su ma jihohi da ma ƙananan hukumomi.
Discussion about this post