Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta dakatar da shirin tallafin N-Power, har sai yadda hali ya yi.
A ranar Asabar ce aka dakatar da shirin, wanda gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta ƙirƙiro cikin 2016, a ƙarƙashin Shirin Inganta Rayuwar Al’umma, wato NSIP, domin bunƙasa rayuwar matasa.
Duk da cewa an jinjina wa yadda shirin ya yi tasiri, kuma ya na ɗaya daga cikin shirye-shiryen da marasa galihu suka ci moriyar sa a ƙarƙashin gwamnatin Buhari, ita kuwa Ministar Harkokin Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa, Betta Edu, ta yi zargin cewa akwai asarƙala da daƙa-daƙa wajen aiwatar da shirin.
A lokacin da Minista Edu ke bayani a wata tattaunawa da aka yi da ita a gidan talabijin na TVC News, a ranar Asabar, ta ce dakatar da shirin na da alaƙa da wata assarƙala da aka bankaɗo.
Asarƙalar Da Aka Gano A Shirin N-Power:
Edu ta ce an binciki wasu daga cikin waɗanda suka ci moriyar shirin amma ba a same su inda aka rubuta cewa a can ɗin suke ba.
“Tilas sai mun bibiyi tsarin N-Power domin gano yadda aka gudanar da shi a baya, domin mu gano irin matsalolin da ke tattare da shirin. Dalili kenan muka dakatar da shirin, har sai mun kammala binciken yadda aka kashe kuɗaɗen tukunna.” Inji ta.
Muna kuma so mu san shin mutane nawa ne waɗanda ke a kan tsarin na N-Power a halin yanzu, mutum nawa ke bin bashi da kuma nawa su ke bi bashi.”
Ta ce gwamnati ta shirye sake yi wa shirin garambawul, kuma za a faɗaɗa bincike har kan yadda ake kashe kuɗaɗen da yadda ake kassafa su, tun daga farkon kafa shirin N-Power.
N-Power shiri ne da aka riƙa ɗaukar matasan da suka kammala karatu ana biyan su N30,000 matsalayin alawus na tallafin aikin wucin-gadin da gwamnatin tarayya ta ɗauke su.
Discussion about this post