Tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu inda za shi, ya na nan a Najeriya daramdam.
Hakan amsa ne da mataimakin shugaban kasan ya bada yayin da wasu ke ikirarin cewa zai kauce daga Najeriya bayan rashin nasara da ya yi a shari’ar zaɓen shugaban kasa a makon jiya.
Atiku ya yi hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Ya ce yana nan zai cigaba da gwagwarmayar kwato wa ƴan Najeriya ƴanci sannan da tabbatar da ganin ɗorewar dimokuraɗiyyar a Najeriya.
“Ni da jam’iyyata, mun wuce matakin zaɓe da kotu yanzu tunda kotu ta yanke hukunci. Sai dai kuma, ba zan je ko’ina ba. Matukar ina numfashi zan ci gaba da fafutuka, tare da sauran ƴan Najeriya, don zurfafa dimokuradiyya da bin doka don cigaban ƙasa baki ɗaya.
Atiku ya yi kira ga matasa da su kara zage damtse wajen shiga a dama da su a siyasa da mulkin kasa.
“Ya kamata a yanzu matasan Najeriya su shiga gaba wajen haka domin sune manyan gobe.
Discussion about this post