Tsohon shugaban APC Sanata Abdullahi Adamu ya yi karin haske game da takarar Ahmed Lawan a zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar APC.
Adamu ya ce shine dai shugaban jam’iyya a lokacin zaɓen fidda gwani amma kuma ba shi kaɗai bane ya fidda sunan Ahmed Lawan ya yi takarar shugaban kasa.
” Ana ta surutu cewa ni ne na zaɓi Ahmed Lawan ya yi takarar shugaban kasa a lokacin da jam’iyyar APC za ta yi zaɓen fidda gwani. Amma kuma abinda ba a sani ba shine kawai don ina shugaban jam’iyya sai in ce ga wanda zai yi takara.
” Akwai wasu da dama da ba a san su ba wanda da sune aka kitsa lallai Ahmed Lawan ya fito takarar fidda gwani. Ba ni kadai bane. Amma duk wanda ya kware a siyasa, ya san ba zai taba yiwuwa hakan ya faru ba.
Adamu ya kara da cewa da shine ya ke yi da hakan za a yi domin ɗan Arewa ya ke so ya zama ɗan takarar APC ba ɗan kudu ba. Sai dai kuma gwamnoni sun zo da nasu bukatar a lokacin cewa lallai mulki ta koma kudu.
” Ni fa ko a lokacin zaɓe na, gwamnoni sun yi adawa da haka, ba su saka suna na ba a sunayen mutum 10 da aka mika wa shugaba Buhari a wancan lokacin, Buhari da kansa ya zaro biro a aljihunsa ya rubuta sunana.
Korafin su shine wai najeriya na tsufa da yawa ba zan iya rike jam’iyyar ba
Discussion about this post