Rundunar Ƴan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa jami’anta sun kama wata matar aure Khadija Adamu dake da shekaru 18 da laifin kashe ‘yar kishiyarta ƴar shekara biyar Hafsat Garba ta hanyar yi mata dukan tsiya.
Khadija ta lakadawa Hafsat dukan tsiya saboda wai da narka bahaya a jikinta.
Sai dai kuma wannan duka ya zo da karewar kwana, Hafsat ba ta rayu ba.
An samu tabbacin mutuwar Hafsat ne bayan likitocin asibitin Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) sun tabbatar da haka.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Auwal Muhammad ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata a garin Bauchi.
A hannun jami’an tsaro Khadija ta amsa laifin da ake zargin ta da aikatawa sai dai ta ce ta lakadawa Hafsat duka ne domin nuna mata laifin da ta aikata.
“Hafsat ta wuce shekarun da za ta rika yin bahaya a cikin wando. Dalilin da ya s kenan na yi mata dukan tsiya da igiyan cajin wayar.
Khadija ta musanta zargin da mutane ke yi cewa ta kashe Hafsat ne saboda kishi.
“Ban kashe Hafsat saboda kishi ba saboda ina da wani dan da na haifa sannan ina da cikin wata hudu da zan haifa na biyu. Allah dai ya yi cewa nice ajalinta.
“Duk ‘yan uwa sun yafe mun laifin da na aikata sannan ina rokon mutane su yi min afuwa su gafarce ni.
Khadija ta roki jami’an tsaron da su sake ta domin ta koma gida ta kula da danta karamin da cikin da ta ke ɗauke da shi.
Ɗan sanda Muhammed ya ce doka za ta yi aiki a kanta kuma da zarar an kammala bincike za su kai ta kotu don a yanke mata hukunci.
Discussion about this post