Rikicin Nijar ya ɗauki sabon salo, bayan da tun a cikin makon jiya hasalallun masu nuna ƙin jinin ƙasar Faransa suka fara zanga-zangar neman ficewar sojojin Faransa daga Nijar, sai kuma Jakadan Faransa da ke Nijar, shi ma su ka ce tilas ya ce, ba su son ganin sa.
A ranar Asabar dubun-bubatar masu goyon bayan juyin mulki sun yi dafifi a wajen harabar sansanin Sojojin Faransa, su na kiran Jakadan Faransa da sojojin duk su dice masu da cikin Nijar.
Aƙalla akwai sojojin Faransa 1,500 a cikin Nijar. Haka kuma cikin makon da ya gabata ne Nijar ta bada sanarwar sallamar Jakadan Faransa da ke birnin Yamai.
To sai dai kuma Faransa ta ce ba zai fita ba, kuma ita ba za ta bi umarnin mahukuntan mulkin sojan Nijar ba.
Faransa ta ce ita har yanzu gwamnatin Mohammed Bazoum da aka hamɓare suka sani, ba gwamnatin sojojin mulki ta Abdourahmane Tciani ba.
Wannan matsaya da Faransa ta ɗauka ta harzuƙa al’ummar Nijar, waɗanda dubun-bubatar su su ka fito yin zanga-zangar.
A ranar Asabar dai an shirya fita zanga-zangar ƙarfe 3:30 na yamma. Amma azarɓaɓi da ɗoki ya sa dubun-bubatar hasalallu sun fita tun ƙarfe 10 na safe.
An yi dafifi a ƙofar sansanin sojojin Faransa 1500, ana rera kururuwar su fice daga Nijar, ba a buƙatar su.
Bayan sun gaigaya wa ƙasar Faransa, sojojin ta da jakadan ta baƙaƙen kalamai, an kuma yanka wani tauren ɗan akuya a wurin, wanda aka yi wa fentin ƙasar Faransa.
Masu zanga-zangar kuma sun riƙa tafiya ɗauke da makara masu fentin launin tutar ƙasar Faransa.
Masu zanga-zangar dai sun riƙa cewa sun gaji da shiga-sharo-ba-shanu da katsalandan ɗin da Faransa ke yi a cikin sha’anin harkokin cikin gidan Nijar.
Ƙungiyoyin kare haƙƙi daban-daban masu adawa da girke sojojin Faransa a Nijar ne su ka shirya zanga-zangar, kuma mutane su ka amsa kiran fitowa da babbar murya.
Shi dai Shugaban Faransa Emmanual Macron, ya na goyon bayan Mohammed Bazoum da gwamnatin sa da aka hamɓaras.
Ita kuma Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar ta ce Faransa na shafa mata kashin kaji ta hanyar muzanta ta, don kawai ta ci gaba da yi wa Nijar ƙarfa-ƙarfa.
Hasalallun masu zanga-zanga dai sun riƙa farautar Jakadan Faransa da ke Yamai, Sylvain Itte, su na cewa ya fito ya kama hanyar gida, tunda gwamnatin soja ta ba shi wa’adin ficewa daga ƙasar.
Zanga-zangar da ta gudana a ranar Asabar ta fi ta ranakun baya zafi, domin sai da hasalallu su ka keta shingayen da ‘yan sanda da sojoji suka kakkafa.
Tuni dai ƙasashen Burkina Faso da Mali su ka kori sojojin Faransa bayan sojoji sun yi juyin mulki a ƙasashen biyu.
Discussion about this post