Alamomin saɓani ko rashin jituwa ya faru tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Zamfara, yayin da Gwamna Dauda Lawal na jihar ya fito ya yi zargin cewa Gwamnatin Tarayya na tattaunawa a asirce tsakanin ta da ‘yan bindiga.
Gwamna Lawal ya yi zargin cewa wasu jami’an gwamnatin tarayya na tattauna cimma wata yarjejeniyar sulhu da ‘yan ta’adda a cikin Jihar Zamfara, ba tare da sanin sa ba.
Gwamnan na Zamfara wanda ɗan PDP ne, ya na sahun gaban caccakar ‘yan bindiga, kuma bai yarda a yi zaman sulhu da su ba.
Ya ce ya samu rahotannin da suka tabbatar da cewa wasu jami’an gwamnatin tarayya na tattaunawa da gungun ‘yan ta’adda daban-daban a ƙananan hukumomi daban-daban na Jihar Zamfara.
Daga nan sai Lawal ya yi kira da a yi bincike mai zurfi domin a gano irin abin da ke faruwa tsakanin waɗannan jami’ai da kuma ‘yan bindiga.
“Rahoto ya zo min cewa wata tawaga daga hukumomin gwamnatin tarayya ta na bi cikin Jihar Zamfara, ta na ganawa da ‘yan bindiga, ba tare da masaniyar Gwamnatin Zamfara ba.”
Haka ya bayyana a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna, Sulaiman Idris.
Ya nuna rashin jin daɗin yadda jami’an gwamnatin tarayya za su shigo Jihar Zamfara ba tare da tuntuɓa ko masaniyar sa ba, sannan kuma su riƙa bi ƙananan hukumomi su na zama da ‘yan bindiga.
Ya ce bai ji daɗi ba jin cewa wasu bangarorin jami’an tsaron a Jihar Zamfara na ba a sanar da su ba.
“Gwamna Dauda Lawal na kira ga Gwamnatin Tarayya ta bincike yadda wasu ɓatagari ke yi wa yaƙi da ‘yan bindiga zangon ƙasa.”
Discussion about this post