Wata kotu a Amurka ta umarci Jami’ar Jihar Chicago ta bai wa Atiku Abubakar takardun shaidar karatun Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a cikin kwanaki biyu.
A ranar Talata ce 19 Ga Satumba ta bayar da wannan umarni.
Kotun ta Gabacin Illinois, ta umarci Jami’ar Chicago cewa ta bayar da kwafe-kwafen dukkan takardun bayanan da Atiku ya nema.
Mai Shari’a Jeffrey Gilbert na Kotun Majistare ne ya bada umarnin a ranar Talata.
Atiku ya shigar da ƙarar neman kotu ta sa jami’ar ta ba shi takardun tun a ranar 2 Ga Agusta.
Neman takardun dai na daga cikin kwatagwangwamar shari’ar zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 Ga Fabrairu, 2023, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta ce Bola Tinubu na APC ne ya yi nasara.
Atiku wanda ya zo na biyu da Peter Obi wanda ya zo na ɗaya, sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, kuma su ka garzaya kotu.
Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jaddada nasarar Tinubu, wanda hakan ya sa Atiku da Obi garzayawa Kotun Ƙoli.
Atiku ya ce ya na so Jami’ar ta ba shi kwafen takardun shaida na Tinubu na asali, domin a Najeriya kwafen shaidar biyu ne ke yawo, kuma sun sha bamban da juna.
Atiku ya ce akwai wanda ke ɗauke da ranar 27 Ga Yuni, 1979 da kuma mai ɗauke da ranar 22 ga Yuni, 1979, dukkan su dai su na ɗauke da shaidar kammala Difiloma da Tinubu ya yi.
Atiku kwafen takardun biyu sun sha bamban, baya ga bambancin rana, akwai bambancin rubutu, bambancin tambari da kuma bambancin sa hannu.
A kan haka ne ya ce don haka idan ba orijinal Tinubu ya bayar ba, to bai cancanta ya tsaya takara ba kenan.
Can a kotun Amurka kuwa, kwana ɗaya bayan ƙarar da Atiku ya shigar ta neman a ba shi kwafen takardun shaidar Tinubu, sai lauyoyin Tinubu su ka nemi kotu ta shigar da Tinubu cikin shari’ar.
Tinubu ya ce batun neman kwafen takardun shaidar na sa da Atiku ke yi bai taso ba, domin maganar ba ta cikin bayanan ƙarar da Atiku ya shigar kan rashin yarda da nasarar Tinubu a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a Najeriya.
Sai dai Atiku ya shaida wa kotun Amurka cewa ai Kotun Ƙoli za ta iya amincewa ya shigar da ƙarin hujjoji kamar yadda Dokar Zaɓen Najeriya ta 2022 ta tanadar.
Kotun Amurka ta ce ta amince da buƙatar Atiku, don haka ta umarci Jami’ar Jihar Illinois ta ba shi kwafen takardun shaidar Difiloma ɗin TInubu a cikin kwanaki biyu, domin ya tantance.
Kwafe-kwafen Takardun Da Jama’ar Illinois Na Tinubu Da Kotu Ta Ce A Gaggauta Bai Wa Atiku:
1. Ainihin kwafen satifiket na kammala Difiloma ɗin TInubu a 1979.
2. Diflomar da Tinubu ya yi kwas a kan ta, a 1979.
3. A haɗa wa Atiku da kwafen shaidar kammala Difiloma na wani daban, wanda ke da irin tambari, hatimi da sa hannu irin wanda na Tinubu ke ɗauke da shi.
Discussion about this post