Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya shigar ƙara a Kotun Ƙoli, inda ya rashin amincewa da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke, wanda ta jaddada nasarar da Bola Tinubu na APC ya yi.
Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa mai Alƙalani biyar, ta ce Atiku ya kasa bayar da hujjojin da kotun za ta ƙwace nasara daga hannun Tinubu.
Kuma ta ce Atiku ya kasa gabatar da hujjojin da kotu za ta gamsu cewa INEC ta yi maguɗi yayin gudanar da zaɓen.
Atiku ya gabatar wa Kotun Ƙoli dalilai 35, tare da cewa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ba ta yi masa adalci ba.
A ƙarar da ya shigar ta hannun lauyoyin sa, bisa jagorancin Babban Lauya Chris Uche, Atiku ya zargin alƙalai biyar da su ka yanke hukunci cewa sun ci mutuncin sa a bayanin yanke hukuncin da su ka yi, inda aka riƙa gaigaya masa kalamai na cin fuska da rashin ladabi a matsayin su na alƙalai.
Ya ce hakan da su ka yi masa kuwa sun nuna son rai da ɓangaranci yayin yanke hukuncin da su ka yi ɗin.
Haka nan Atiku ya ce alƙalan biyar a ƙarƙashin Haruna Tsammani, ba su bi zarge-zargen da ya yi sun tsefe tare da ƙwalailaice su ba.
Ya ce sun tafka kuskure wajen sake jaddada wa Tinubu nasara.
Ana dai sa ran shi ma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi zai shigar da ta sa ƙarar a Kotun Ƙoli, kafin wa’adin kwanaki 14 ya wuce.
Discussion about this post