Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta bayyana cewa ta kama wani tsoho mai shekara 63 John Mahanan bisa laifin yi wa yara kanana mata masu shekaru 4 zuwa 8 fyade a kauyen Mabel dake karamar hukumar Butura.
Baya ga wannan dattijo rundunar ta kama wasu batagari 25 a jihar bisa laifin fyade, garkuwa da mutane, fashi da makami da dai sauran su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Julius Alawari ya sanar da haka a hedikwatar rundunar dake garin Jos.
Ya ce a ranar 22 ga Agusta ne mahaifin yaran Lucky Luka ya kai kara a ofishin ‘yan sanda dake kauyen Mabel cewa a ranar Mahanan ya yi wa ‘ya’yansa mata biyu Retyit Lucky mai shekara 4 da Loveth Nehemiah mai shekara 8 fyade a cikin gidansa.
“Mahaifin ya ce Mahanan ya yi lalata da wadannan yara a lokacin da suke ke gidansa wasa.
“Sakamakon gwajin da likitoci suka yi a asibitin Cottage ya nuna cewa an yi lalata da wadannan yara.
Bayan haka kwamishinan ya ce rundunar ta kama Salisu Adamu mai shelara 30 dan asalin kauyen Minta dake karamar hukumar Bassa dake da alaka da yin garkuwa da dalibai 7 na jami’ar Filato.
Ya ce binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa Adamu na daga cikin fursinonin da suka gudu daga gidan yari na Jos a shekarar 2020.
“Adamu ya tabbatar cewa yana daga cikin maharan da suka yi garkuwa da daliban jami’ar.
Alwari ya ce rundunar ta fara farautar sauran abokan aikin Adamu domin ganin an kamo su Kuma an yanke musu hukunci.
Ya kuma ce ‘Yan sanda sun kama Shammah Emmanuel wanda aka fi Sani da ‘Hitman’ mai shekara 20 da Joseph Seth wanda aka fi Sani da ‘Small Seth’ dan shekara 19 ‘yan fashi da makami a maboyar su dake Angwan Mata a Gada-Biu.
“Wadannan matasa sun shahara wajen yi wa mutane fashi da makamai a Gada-Biu da Rukuna Road dake karamar hukumar Jos ta Arewa.
Alwari ya ce an kama wadannan mutane da bindiga karama na hannu.
Discussion about this post