Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa dakarun ta sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a kauyen Kuregu dake karamar hukumar Zaria.
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar Mansir Hassan ya sanar da haka a Kaduna.
Hassan ya ce dakarun sun ceto wadannan mutane ranar Asabar bayan samun bayanan siri tare da yin sintiri da jami’an tsaron suka yi a hanyar Galadimawa dake karamar hukumar Giwa.
“ Dakarun sun ci gaba da tsananta kai hare-hare a dazukan dake hanyar Galadimawa wanda hakan ya sa masu garkuwa da mutanen suka gudu suka bar mutanen da suke tsare da su.
“ Rundunar na zargin cewa wani makusancin mutanen da aka yi garkuwa da su ne ya hada baki da kungiyar shahararren mai garkuwa da mutane marigayi Isah Danwasa wanda wanda hakan sa aka yi garkuwa da mutanen.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Musa Garba ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hada hannu da jami’an tsaro domin yakan aiyukkan mahara sannan ya tabbatar cewa rundunar za ta ci gaba da kokari wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar.
Discussion about this post