Akasarin ma’aikata a ofisoshin Ma’aikatun Gwamnati, Cibiyoyi da Hukumomi da kuma bankuna sun amsa kiran Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), sun tsunduma yajin aikin gargaɗin kwanaki biyu da ƙungiyar ta umarci a fara.
Sun shiga yajin aikin domin nuna damuwar su kan raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fuskanta, tun bayan cire tallafin fetur.
Ofisoshin da wakilin mu ya gani a garƙame su na da yawa a Abuja, inda yawancin manyan ƙofofin shiga ma’aikatu duk su ka kasance a kulle.
A Sakateriyar Gwamnatin Tarayya a Abuja ma rarai ta ke, babu ma’aikata, sai ‘yan ƙalilan.
Haka kuma wakilin mu ya ga babbar ƙofar shiga Hedikwatar Ma’aikatar Yaɗa Labarai, wadda aka fi sani da Radio House, ita ma a garƙame da kwaɗo, masu yajin aiki sun hana shiga ciki.
Wasu bankuna da dama ba su buɗe ba a Abuja kamar Access Bank, First Bank na Nyanya da Union Bank na Area 3, duk ba a buɗe su ba.
Waɗanda su ka buɗe wani reshe na su, kamar Guaranty Trust Bank kuwa, babu hada-hadar jama’a sosai a ciki.
A ranar Asabar ce NLC ta bayyana cewa za ta fara yajin aikin sai-baba-ta-gani nan da makonni biyu, ko kwanaki 21, bayan kammala yajin aikin gargaɗi na kwana biyu.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za su a yi gagarimin yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu, kafin ta fara yajin aikin game-gari nan da kwanaki 21, domin nuna rashin jin daɗin yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa bijiro da hanyoyin magance ƙalubalen da ke tattare da cire tallafin fetur.
NLC ta ce za a yi yajin aikin ne a faɗin ƙasar nan, a ranakun 5 da 6 Ga Satumba.
Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero ne ya bayyana haka, a ranar Juma’a, lokacin da ya ke taron ganawa da manema labarai, Hedikwatar NLC da ke Abuja.
Ya bayyana cewa sun yanke shawarar cewa za a tafi yajin aikin, saboda gwamnatin tarayya har yau ta ƙi cika alƙawarin da ta ɗauka a tarukan baya su ka yi.
“NLC ta amince dukkan ma’aikatan faɗin ƙasar nan su tafi yajin aiki nan da kwanaki 21ko makonni biyu, bayan kammala yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu, har sai Gwamnatin Tarayya ta fito da tsare-tsaren sauƙaƙa wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwar da ke addabar su a ƙasar nan.
“Za mu fara da yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu tukunna, a ranakun 5 da 6 Ga Satumba. Daga nan kuma sai mu sanar da fara yin dogon yajin aiki nan da kwanaki 14 ko 21 masu zuwa.”
Idan ba a manta ba, a farkon Agusta ne NLC da TUC su ka gudanar da zanga-zanga a Abuja, inda su ka bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya shammaci ‘yan Najeriya, ya cire tallafin fetur, a lokacin da ‘ƙaramin ƙaramin albashin Naira 30,000 ko tankin Keke NAPEP ba zai cika ba’.
A lokacin waccan zanga-zangar, Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin NLC da TUC na Jihar ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya shammaci ‘yan Najeriya, ya cire tallafin fetur ana tsakiyar murnar rantsar da shi.
Ya ce tun daga lokacin ya ƙara tsunduma ‘yan Najeriya cikin raɗaɗi da ƙuncin tsadar rayuwa.
Shugaban na Jihar Enugu ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin zanga-zangar game-gari da aka karaɗe ƙasar da ita, domin nuna wa sabuwar gwamnatin Tinubu irin matsanan halin ƙuncin da ake ciki a faɗin nan.
Da ya ke magana dangane da cire tallafin fetur ba zato ba tsammani, Fabian Nwigbo na NLC da takwaran sa na TUC Ben Asogwa, sun ja zugar masu zanga-zanga har Gidan Gwamnatin Enugu, inda Mataimakin Gwamna, Ifeanyi Ossai da wasu jami’an gwamnati.
Sun ce sun je Gidan Domin su isar da saƙon su ga Shugaba Bola Tinubu, ta hannun Gwamna Peter Mbah.
“Shugaba Bola Tinubu ya shammaci ‘yan Najeriya, yayin da ya janye tallafin ana cikin rantsar da shi, lokacin da aka shagala cikin murnar hawan sa mulki.
“Ya cire tallafin fetur, amma har yanzu ba a ƙara wa ma’aikata albashi ba. Yanzu ƙaramin albashi na Naira 30,000, ko tankin Keke NAPEP ba zai iya cikawa ba.”
A Abuja kuwa, NLC da TUC sun ce laƙanin Naira 8,000 ga marasa galihu cin fuska da raina talakawa ne.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC, ta bayyana cewa raba wa talakawa tallafin Naira 8,000 a mawuyacin halin da aka jefa ‘yan Najeriya a ciki, “cin fuska ne da raina masu wayau.”
Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a ranar Laraba, a cikin saƙon da ya aika wa ma’aikata, a Abuja, lokacin da ya ke jawabi a wurin zanga-zanga.
“Raba wa talakawa marasa galihu Naira 8,000 a wannan halin cin fuska ne a gare su, kuma an raina masu wayo. Mu na kira ga Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da muka yi da ita, wadda idan aka yi aiki da ita za ta zama alfanu ga talakawa a faɗin ƙasar nan.”
Bayan cire tallafin fetur, gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta fito da wasu tsare-tsaren sauƙaƙa ƙuncin rayuwa ga talakawan ƙasar nan da ma’aikatan gwamnati masu ƙaramin ƙarfi.
Sai dai kuma akasarin masu bayyana ra’ayin su na ganin cewa duk da tallafin ya yi kaɗan, to ba zai kai ga waɗanda su ka fi cancanta su ci moriyar sa ba.
Sannan kuma a sama da talakawa miliyan 100, za a bayar da tallafin ne ga mutum miliyan 12 kaɗai.
Sannan kuma wani bayani da Wale Edun ya yi a lokacin tantance shi minista, ya ƙara sa guyawun talakawa sun yi sanyi.
Edun cewa ya yi duk zafin talaucin mutum, ba za a ba shi tallafin na Naira 8,000 ba, sai ya na da asusun ajiyar kuɗaɗe a bankuna.
“Maganar tallafin nan duk shafa-labari-shuni ce. Har an shiga wata na uku kenan da cire tallafin fetur, amma ba a bayar da tallafin ko sisi ba. Babu wani ma’aikacin da ya samu tallafin Naira 1 tal daga gwamnati. Kuma har yanzu babu ma alamar motocin da aka ce za su samar da sassaucin kuɗaɗen zirga-zirgar ko guda ɗaya.” Haka Ajaero ya ja jaddada.
Ya ce kada Shugaba Tinubu ya shiga sahun shugabanni masu cika mutane da nuna damuwar su kan matsaloli kaɗai.
“Ya kamata Shugaban Ƙasa ya tashi tsaye ya sa a kamo manyan ɓarayin gwamnati da suka sace mana kuɗaɗe, su dawo da su.”
Haka shugaban na NLC ya bayyana a fusace.
Ya ce bayan wannan zanga-zangar, za su je su yi nazarin abin da zai biyo baya. Wannan inji shi zai bayar da ƙofar tafiya yajin aiki, idan gwamnati ba ta yi komai a kai ba.
Discussion about this post