Gwamnatin Tarayya ta roƙi Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta janye batun tafiya yajin aikin kwanaki 21, maimakon haka, ta ba ta makonni biyu domin kammala tsare-tsaren cika alƙawurran da aka ɗaukar wa NLC amma ba a cika ba.
Ministan Ƙwadago, Simon Lalong ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke yi wa manema labarai ƙarin bayani, bayan ganawar sirrin da ya yi da Gamayyar Ƙungiyoyin Ƙwadago na TUC, ranar Litinin a Abuja.
Lalong ya ce ya kira taron ne domin gaggauta dakatar da gagarumin yajin aikin gargaɗi da NLC ta shirya yi a ranar Talata da Laraba.
NLC ta shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi a yau Talata da Laraba, domin nuna rashin amincewa da cire tallafin fetur, ba tare da bijiro da hanyoyin sauƙaƙe raɗaɗin tsadar rayuwa ba.
Ta kuma shirya zarcewa da yajin aikin kwanaki 21 cur.
Sai dai kuma taron wanda Minista Lalong ya kira, shugabannin NLC ba su halarta ba. Lamarin da ake ganin da wahala taron ya yi wani tasiri.
A na ta ɓangaren, TUC ta ce tafiya yajin aikin na gargaɗi ba shi da wata fa’ida. Maimakon haka, sai TUC ta ce ta amince ta zauna da gwamnati domin a tattauna inda matsalolin su ke.
Lalong ya ce gwamnati ta za magance matsalolin a cikin makonni biyu, sannan a koma a ci gaba da tattaunawa kan teburin tattaunawa.
“Wasu abubuwan da mu ka tattauna akwai masu buƙatar aiwatarwa a cikin gaggawa. Akwai kuma waɗanda ke buƙatar tsawon lokaci tukunna. To wannan ne dalilin tattaunawa da muka yi da TUC.
“Mun amince kada a yi gaggawar tafiya yajin aiki a cikin makonni biyu masu zuwa da mu kuma za mu je mu yi dukkan abin da ya dace.”
Shugaban TUC shi ma ya bayyana ƙorafe-ƙorafen da ya ce sun yi wa gwamnati, dangane da halin da ake ciki.
Discussion about this post