Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba Abdullahi Usman ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata matar aure Hajiya Kara’atu Tanimu a Nasarawa dake Jalingo.
Usman ya ce maharan sun sace Kara’atu bayan mako daya da mahara sun yi garkuwa da matar shugaban ‘yan sanda a Mile-Six dake jihar.
Da yake ganawa da manema labarai ranar Juma’a kakakin rundunar ya ce maharan sun yi awon gaba da Kara’atu ranar Alhamis a gidan mijinta Alhaji Tanimu Rabi’u.
“A lokacin da suka shiga gidan Alhaji ya yi tafiya zuwa kasar Saudiya da hakan ya sa suka tafi da matarsa, wayoyin ta da kudin naira 11,000.
Usman ya ce tuni jami’ai su suka fantsama farautar maharan.
Discussion about this post