Lantarki ya yi ajalin wani barawon wayoyin na’urar tiransifoma a safiyar Juma’a a cikin harabar wani kamfani dake Minna a jihar Neja.
Ma’aikatan Kamfanin ne suka tsinci gawar barawon manne a jikin na’urar.
Shugaban sashin shari’a na kamfanin raba wutar lantarki na Abuja, AEDC, Aminu Ubandoma, ya tabbatar da haka wa manema labarai a garin Minna.
Ubandoma ya ce ba tun yanzu ba ake ta daga cikin tiransifoman da ke wannan kamfani.
Ya ce Kamfanin AEDC za ta hada hannu da jami’an tsaro domin kawo karshen sace-sace wayoyi da ake yi.
Bayan haka kakakin rundunar ƴan sandan jihar Wasiu Abiodun shima ya tabbatar da haka wa manema labarai.
Abiodun ya ce an tsinci abin yankan waya sannan da wasu wayoyin wutan lantarki da ya sace a wurin da ya mutu.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da bincike tare da neman ƴan uwan mamacin.
Discussion about this post