An bankaɗo yadda Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta sayar jiragen ruwa 16 a kan Naira miliyan 156 kacal a cikin 2019.
Jiragen ruwan da aka sayar mallakar Gwamnatin Tarayya, akwai ML Pategi wanda aka sayar arha takyaf Naira miliyan 3.2; an kaɗas da ML Misau a kan farashin arha ta fi bashi, kan Naira miliyan 1. da ɗoriyar Naira 60,000.
Shi kuwa PB Kabba, duk da gingimemen girman sa, Naira miliyan 5.4 aka kaɗa masa ƙararrawa, wani ya lale kuɗi ya biya.
Shi kuwa SPB 3 bayar da shi aka yi a tukuicin naira 54,000, sai PC Shelleng wanda aka saya kan tukuicin naira 48,000 kacal.
Kwamitin Bincike na Majalisar Tarayya ne ya fara binciken Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa dangane da wannan mummunar aika-aika, wadda aka yi a cikin 2019.
Takardun bayanai da ke a gaban kwamitin sun nuna cewa an yi gwanjon motocin alfarma irin su Ranger Pick-up, Toyota Coaster da dama, wasu motocin masu yawa ƙirar Toyota Corolla, sai Toyota Hiace masu yawa, Toyota Camry Salon da wasu zunduma zunsuman motoci na alfarma masu yawa a kan farashi arha takyaf.
Kwafen takardun bayanai kuma dai sun nuna a cikin 2022 an sayar da kayayyaki har miliyan 45 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa a kan Naira 1 kowane kaya ɗaya.
Gaba ɗaya farashin kuɗin kayan guda miliyan 45, ya kama Naira miliyan 45 kenan aka karɓa.
An sayar da kayan a matsayin ƙarambosuwa, kamar yadda rasiɗin sayar da kayan wanda aka rubuta a ranar 9 Ga Agusta, 2022 ya nuna.
NPA ta kuma sayar da wasu kayayyaki guda miliyan 10 da 800,000 a Apapa Dockyard CIkin 2021, akan Naira 1 kowane. Jimillar kuɗaɗen sun tashi Naira miliyan 10.8 kenan.
Kwafen takardun sun nuna an sayar da kayayyaki guda miliyan 20 a Tashar Jiragen Ruwa ta ll a Apapa da ke Kirikiri, kan Naira 1 kacal kowane. An karɓi Naira miliyan 20, a matsayin kayan ƙarambosuwa ce.
Shugaban Kwamiti Julius Ihonvbere, ya ɗage zaman kwamiti zuwa ranar Laraba, 25 ga Satumba, domin jami’an NPA su gabatar da amsoshin tambayoyin da aka yi masu, tare da kai kwafen takardun yadda aka yi yarjejeniyar yanka wa kayan farashi da kuma yadda aka yi cinikin.
An kuma umarci jami’an NPA su kai wa Majalisa kwafen takardun kamfanonin da su ka nemi tandar cinikin kayan, da kuma yadda aka buga tandar neman masu buƙatar saye.
Discussion about this post