Akalla gaggan ƴan ta’adda da su ka yi fice, su ka yi suna wajen sace mutane da amsar miliyoyin kudin fansa da kuma kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba, su bi su har gida su kashe ne suka yi zaman musamman na neman sulhu da tawagar gwamnatin tarayya da rana tsaka Katsina.
PREMIUM TIMES ta gano cewa waɗannan manyan ‘yan ta’adda bakwai na daga cikin wadanda suka halarci taron sulhu da jami’an gwamnatin tarayya a jihar Katsina.
Majiya sun shaida mana cewa an yi wannan zama ne a Fankama, dake jihar Katsina.
A cikin jawabin da jagoran gwamnatin tarayya ya yi, an ji yana cewa gwamnati na rokon ‘yan ta’addan su dakatar da sace mutane da su ke yi, sannan da kisa da su kan bi mutane har gida su kashe da kuma karbar kuɗin fansa.
Haka kuma wani soja da baya so a fadi sunan sa saboda ba a bashi damar yin magana a kai ba ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa “Zan iya tabbatar da cewa an gudanar da taron kuma an gudanar da wasu tarurruka da dama a jihar Zamfara,” Ya ce tawagar gwamnatin tarayya ta gana da wasu sojoji a jihar Katsina kafin su wuce zuwa karamar hukumar Faskari inda taron ya gudana. Muna ɓoye sunansa ne saboda an hana shi yin magana da manema labarai kan ci gaban.
Shugabannin ‘yan ta’addanci bakwai da suka halarci taron sun hada da Ado Aleiro, Yusuf Yellow, Masume, Alhaji Bandi, Alhaji Kabiru, Goma tashin like da Idi Muwange. Majiyar biyu da PREMIUM TIMES ta zanta da su a lokaci daban duk sun ambaci sunayen sarakunan guda shida.
A daya daga cikin faifan bidiyo da PREMIUM TIMES ta gani wanda aka yi jawabi a harcen Hausa, an ga Aleiro yana zaune tare da wasu manyan ‘yan ta’adda a lokacin da ake wannan taro.
Aliero ya taba shaida wa BBC cewa shi baya satan mutane, Kashe mutane ya ke yi.
Yellow dan uwan Aliero ne wanda shima yana da na shi baradan da ke masa aikin kisa da sace mutane. Shine ke rike da yankin Tsafe, kuma a nan ne ya ke aikata tabargazar sa.
Shi kuma Goma tashin like, shine ke aikata bala’in sa a yankin Bilbis, jihar Zamfara da Hayin Gada, yankin Katsina tare da makarraban sa wato yaran sa.
Sai kuma Masume wanda shi aikata ta’addanci a yankin dajin Munhaye sai kuma Muwange wanda shine gogarman da ke ta’addanci a ayankin Fankama. Haka kuma Bandi da Kabiru suma ‘yan ta’adda ne da ke aikata ta’addancin su a yankin dazukan Faskari zuwa Sabuwa.
Idan ba a manta ba gwamnatin Zamfara ta yi korafin cewa gwamnatin Najeriya na tattaunawa da ƴan bindiga ba tare da an saka gwamnatin jihar a cikin abinda ake yi ba.
Amma kuma daga baya Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya ce a yi biris da korafin gwamna Lawal Dare.
Ya ce ita Gwamnatin Tarayya ta na nan kan matsayar ta ta tabbatar da bin duk wasu hanyoyin da su ka dace, waɗanda bin su zai tabbatar da an daƙile tashin hankula kuma an dawo da zaman lafiya a cikin jama’a.
Discussion about this post