Wasu Shugabannin mazabu 9 da mutum sama da 700 sun canza sheƙa daga jami’yyar NNPP zuwa jami’yyar LP a jihar Kaduna.
Dan majalisar dokoki na jihar mai wakiltar Chikun/Kajuru Ekene Abubakar-Adams tare da Shugaban LP na Arewa maso Yamma Umaru Mohammadu suka marabci masu sauya shekar ranar Alhamis a Kaduna.
Shugabannin mazabu da mabiya bayan su 700 sun fito ne daga garuruwan Kujama, Narayi, Sabon-Tasha, Kakau, Sabon-Gari Rido, Nasarawa, Gwagwada da Yelwa inda suke shaida cewa sun fice daga jami’yyar ne domin soyayyar da suke wa Peter Obi da Ekene a Arewa maso Yamma.
Da yake marabtan bakin a ofishin mazabarsa tare da wasu jiga-jigan jami’yyar LP Ekene ya ce shawarar da suka ɗauka ya zo a kan lokaci ganin yadda jami’yyar LP ke kara habbaka a jihar Kaduna .
“Nan ba da dadewa ba masu ruwa da tsaki daga wasu jami’iyyun za su canja sheka zuwa LP dubi da irin kyawawan wakilcin da muka gani daga jami’yyar a yanzu.
Bayan haka shugaban gundumar Kujama Nuhu Aruwa ya ce ba su da Wani zabi da ya wuce mu hada kai da jam’iyyar Labour, dubi da irin ayyukan alheri da Ekene yake yi tun lokacin da ya hau kujerar dan majalisar tarayya.
Discussion about this post