A sanadiyyar halin kuncin rayuwa da ya tsananta a kasar nan, roko ya zame ruwan dare musamman ga ƴan mata ga samarin su.
A cikin wannan hali da ake ciki, roko ya na neman ya hana samari ci gaba da soyayya tsakanin su da ƴan matan su. Da yawa sun shaida cewa abin ya zama kamar sana’a yanzu. Wato mata sun koma mabarata da karfin tsiya.
Wani matashi ya shaida wa wakilin mu a lokacin da suke tattauna wa gane da lamarin cewa ” Bambancin ƴan mata yanzu da almajirai masu rike roba suna ne kawai da kuma rike robar amma rokon iri ɗaya ne yanzu, sun ma fi almajirin jaraban bani-bani.
Samari suna ta kauce wa ƴan matan su, saboda a cewar wasu matan ba su da tausayi.
Mansir Danlami ya ce ” Wannan lamari ya yi tsanani matuka yanzu. Abinda ƴan mata ke yi ya wuce misali. Muma fa abin tare ake faman nan. Daga kana lallaɓa ƴar rayuwar ka sai yarinya ta sa ka a gaba don ka ce kana ƙaunarta. Roko kullum na yau daban da na gobe.
Nazifi Sani cewa ya yi ” Har wata dabara suke da shi yanzu, idan kun fara soyayya, sai a fara da samun kati, samun data, waya ta ta fashe, zan canja screen, daga nan sai ace, ta lalace, daga nan sai zan sake wayar daga nan, zan ci shawarma, gobe nama. Yadda kasan an aiko ta kassara ka, kai baka ci sai lafta mata kawai ka ke yi.
Da yawa daga cikin samari har da manyan maza sun bayyana rashin jin dadi da tausayi da mata yanzu suka dauka.
” Abin tausayi shine, ya kai ga saboda ta ji dadin rayuwa, komai ƴar karamar yarinya na iya yi don ta samu kuɗi.
Sai dai kuma wasu mata da suka tattauna da Wakiliyar mu, sun bayyana cewa yanayin rayuwa ne ya sa matan suka manta gaban su yanzu.
Ko wacce mace na son ta rike Iphone, ta ci shawarma, ta sha Ice cream, kuma bata da kuɗi, ka ga dole ta matsa wa saurayin ta, daga nan sai a faɗa wata hanyar don a samu abinda ake so.
” Yanzu a halin da ake ciki abin ya yi tsanani, ba kasafai mace ke samun yadda ta ke so ba. Idan kika matsa, ya tattara ya kauce. Kin ga kin yi rashi kenan. Dan wanda kike samu, ki daina samu kwatakwata.
Gambo Lawal wani mai rubuce-rubuce kan harkar alaka da soyayya tsakanin mace da namiji, ya ce, ” Tsakani da Allah lokaci ne ya kawo mu haka, mata ba su da hakuri, ba su da kudi sai son su ji dadi. Shawara ta gare su shine su ma su rika sara suna duɓin bakin gatari. Gaba ɗaya ake cikin wannan matsin. Ba komai bane za a rika dole sai an ci ko an rike ba.
Discussion about this post