Shugaba Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro su yi duk irin ƙoƙarin da za su yi domin su tabbatar sun ceto ɗaliban Jami’ar Zamfara da ke Gusau, waɗanda ‘yan bindiga su ka arce da su.
Da ya ke yin tir da ‘yan bindigar, Tinubu ya ce babu wani dalilin da zai sa a kwashe ɗalibai masu jidalin neman ilmi a yi garkuwa da su.
Tinubu ya ƙara jaddada cewa gwamnatin sa ta duƙufa wajen tabbatar da kare kowane ɗan Najeriya.
Daga nan ya tabbatar wa iyayen ɗaliban cewa za a yi duk irin ƙoƙarin da ya wajaba domin a ceto ɗaliban.
Idan ba a manta ba, gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta shafe shekaru takwas ta na bada umarni ga jami’an tsaro su ceto waɗanda ake kamawa a duk lokacin da aka yi garkuwa da mutane, musamman ɗalibai.
Haka kuma Buhari ya shafe shekaru takwas ya na yir tir da Allah wadai ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a duk lokacin da su ka yi ɓarna ta kisa ko garkuwa da mutane.
Kwashe ɗaliban Zamfara da ‘yan bindiga su ka yi, wani babban ƙalubale ne ga Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Badaru da kuma Ƙaramin Ministan Harkokin Tsaro, Bello Matawalle, wanda ɗan Jihar Kebbi ne.
Kafin naɗa Matawalle ƙaramin minista, shi ne Gwamnan Zamfara, wanda ya shafe shekaru huɗu ya na mulki, ba tare da an samu wani ci gaban daƙile matsalar tsaro a jihar ba.
Discussion about this post