Shugaban Kasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon Kwamishinan Kasafin Kuɗin Kaduna Mohammed Sani Abdullahi Dattijo ɗaya daga ciki mataimakan gwamnan babban bankin Najeriya, CBN.
Shugaban kasa Tinubu ya aika da sunayen sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Da mataimakan sa 4 majalisar Dattawa domin tantance su.
Waɗanda aka aika da sunayen su mataimakan gwamnan babban bankin Najeriya sun hada da,
1) Emem Nnana Usoro
(2) Muhammad Sani Abdullahi Dattijo
(3) Philip Ikeazor
(4) Bala M. Bello
Shugaba Tinubu ya aika da sunan Olayemi Michael Cardoso majalisar Dattawa a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya.
Discussion about this post